Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka

Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka

  • Kungiyar Taliban a Afghanistan ta bayyana sabuwar doka ga mata da kuma mutanen kasar
  • Kungiyar ta ce ta haramta kida, sannan mata ba za su yi tafiya mai nisa sai da rakiyar namiji
  • Kungiyar ta kuma bayyana cewa, mata na da damar zuwa aiki, asibiti da kuma makaranta

Afghanistan - Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar da haramta kida a Afghanistan saboda "Ba Musulunci ba ne".

Wannan batu na kunshe ne a cikin wata hira da jaridar New York Times da kakakin kungiyar Taliban, Zabiullah Mujahid, a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta, Ripples Nigeria ta ruwaito.

Sai dai ya lura cewa Taliban na fatan shawo kan mutane su yi biyayya ga sabuwar dokar, maimakon tilasta musu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

Afghanistan: Taliban ta haramta kida da waka bayan karbe mulki
Shugabannin Taliban | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Haramcin zai zama kamar dawo da daya daga cikin tsauraran dokoki na mulkin kungiyar Taliban ta 1990, lokacin da aka hana yawancin nau'ikan kade-kade, ban da wakokin addini.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban mai magana da yawun kungiyar ya sanar da sabon haramcin a wata hira inda yayi kokarin jaddada cewa Taliban ta canza daga tsaurin gwamnatinta na farko.

Zabiullah Mujahid ya fadi cewa

"An haramta kida a Musulunce, amma muna fatan za mu iya shawo kan mutane cewa kar su aikata irin wadannan abubuwa, maimakon tilasta musu."

'Yan Taliban sun halasta wakokin addini a lokacin tsohuwar gwamnatinsu ta farko, amma suna daukar wasu nau'ikan kade-kade a matsayin abin jan hankali wanda zai iya karfafa tunani mara kyau.

Mata ba za su yi tafiya mai nisa sai da rakiyar namiji

Mata a Afghanistan za su bukaci namiji a matsayin dan rakiya don yin balaguron da ya wuce fiye da kwana guda, in ji wani shugaban Taliban.

Kara karanta wannan

Afghanistan: Wata kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban, ta harba makami

Mujahid ya ce gwamnatin za ta kasance mai sassaucin ra'ayi sabanin yadda ta kasance a baya wajen sanya dokoki kan mata kamar yadda ta ke neman karbuwa daga kasashen duniya a yanzu, jaridar Mirror ta ruwaito.

Acewarsa, amma a lokaci guda ya kamata mata su zauna a gida na dan lokaci; ra'ayin da masu sukar Taliban suka ce shine abin da ya faru lokacin da suka yi mulkin farko.

Mujahid ya kuma yi ikirarin cewa mata za su iya ci gaba da aiki muddin sun rufe fuskokinsu.

A karkashin mulkinsu na baya 'yan Taliban sun tilastawa mata sanya cikakkiyar burqa wacce ke rufe kai da fuska da raga da ke rufe idanu.

Kakakin na Taliban ya kuma ce za a bai wa mata damar zuwa makaranta, aiki da asibitoci amma za su bukaci a yi musu rakiya tare da wani namiji ga duk wasu tafiye-tafiye masu nisa.

Afghanistan: Wata kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban, ta harba makami

Kara karanta wannan

Kungiya na bukatar a fattaki NSA, tace harin NDA na nuna lalacewar tsaro

A wani labarin, a saman wani tsauni mai mamayewar bakin haure tsawon shekaru da dama, wasu mayakan dake adawa da mulkin Taliban sun harba babban makami a cikin wani kwari mai zurfi a Panjshir, AlJazeera ta ruwaito.

Mayakan sun kasance mambobi ne na National Resistance Front (NRF) - babbar fitacciyar kungiyar adawa ta Afganistan da ta fito tun lokacin da Taliban ta kame Kabul kwanaki tara da suka gabata.

Tare da mayakan kungiyar da tsoffin sojojin gwamnati masu mukamai, NRF ta kafa buhunan bindigogi, harsasai da wuraren sa ido wadanda aka yi da buhunna cike da kasa don kare farmakin Taliban a sansaninsu da ke a Kwarin Panjshir.

Asali: Legit.ng

Online view pixel