Batun Abba Kyari: Kwamiti ya gama bincike, ya mika rahoto ga Sufeto-Janar

Batun Abba Kyari: Kwamiti ya gama bincike, ya mika rahoto ga Sufeto-Janar

  • Kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar Abba Kyari ya gama bincike, ya kuma mika rahoto ga IG
  • Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan da aka dakatar da Abba Kyari bisa zargin rashawa
  • A halin yanzu, ba tabbatar da menene ke cikin rahoton ba, amma dai an mika shi Sufeto janar na 'yan sanda

Kwamitin Bincike na Musamman ya mika rahotonsa ga Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Baba, makonni biyu bayan da aka umarce shi da ya binciki tsohon Shugaban rundunar IRT kuma Mataimakin Kwamishinan' Yan sanda, Abba Kyari.

Kwamitin na mutum hudu karkashin jagorancin Mataimakin Sufeto -Janar na 'yan sanda mai kula da sashin binciken manyan laifuka na rundunar, Joseph Egbunike, ya mika sakamakon binciken ga IG ranar Litinin 16 ga watan Agusta.

A baya mun rahoto cewa, hukumar FBI ta kasar Amurka ta zargi Abba Kyari da hannu cikin wata damfara da Abbas Ramon (Hushpuppi) ya yi kan wani dan kasuwar Qatar, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

Batun Abba Kyari: Kwamiti ya gama bincike, ya mika rahoto Sufeto-Janar
DCP Abba Kyari | Hoto: Abba Kyari
Asali: UGC

Domin bincika lamarin, IG a ranar 1 ga Agusta ya ba da shawarar dakatar da Abba Kyari ga Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan sanda, daga ranar 31 ga Yuli, sannan ya kafa kwamiti don bincika zargin da ake yi masa.

Yaya zaman ya kasance?

A yayin zaman ta, Kyari ya bayyana sau da dama a gaban kwamitin inda ya yi watsi da zargin hada baki da Hushpuppi don damfarar dan kasuwar na Qatar.

An tattaro cewa zaman kwamitin tare da Kyari ya kasance cikin annashuwa, lamarin da ya baiwa Kyari kwarin gwiwar cewa za a wanke shi daga zargin, in ji rahoton Reuben Abati.

Majiyoyi sun ce Egbunike da Kyari suna da dangantaka ta dogon lokaci tunda tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sanda ne a sashen asusun 'yan sanda inda ya yi aiki sama da shekaru 15.

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamnatin Buhari ta ware wa 'yan sanda kudin sayen man fetur

An gano cewa kwamitin ya gabatar da rahoton a makon da ya gabata amma IG ya ki amincewa da shi saboda ya yi wa Kyari sassauci.

Wata majiya ta ce:

“Kwamitin ya kammala bincikensa sannan ya mika rahotonsa ga IG a ranar Alhamis ko Juma’a da ta gabata amma IG ya ki amincewa. Bai gamsu da sakamakon kwamitin da shawarwarinsa ba."

Sam ba a yi wa Abba Kyari adalci ba: 'Yan Arewa sun koka kan kwace mukamin Kyari

A wani labarin, Hadin gwiwar Kungiyoyin Arewa sun yi zargin cewa cibiyar bincike ta FBI da rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) sun take hakkin Abba Kyari kai tsaye na bincikensa da ake.

A cewar kungiyar, Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda (DCP), ba a ba shi damar yin bayani ba kawai FBI da NPF suka dauki matakin gaggawa a kansa.

Don haka, sun nemi a gaggauta duba dakatarwar Kyari sannan a mika shari'arsa ga Hukumar Leken Asiri ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Karo na hudu, Abba Kyari ya gurfana gaban kwamitin bincike, an kwashe sa'a 4 yana shan tambayoyi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.