Har yaran masu kudi muna kamawa, Shugaban hukumar Hisbah
- Hisbah ta kare kanta kan zargin da ake mata cewa bata kama yaran shugabanni da masu kudi
- Manyan Diraktocin sun yi hira ne da gidan rediyon Freedom dake Kano
- Hukumar Hisbah ta shahara da hukunta masu aikata laifukan da ya suka sabawa tarbiyya
Kano - Hukumar dabbaka koyarwan addinin Musulunci da kuma gayaran tarbiyya watau Hisbah ta jihar Kano ta bayyana usulubin da take bi wajen gudanar da ayyukanta.
Wannan ya biyo bayan soke-soken da ake yiwa hukumar da nuna banbanci tsakanin masu kudi da talakawa wajen yanke hukunci.
A makon da ya gabata, an soki hukumar da dode idanuwa da kunne kan daurin auren diyar Sarkin Bichi da 'dan shugaba Buhari inda hotuna suka bayyana irin kayan da yan mata suka sa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsokaci kan haka, wani dirakta a Hisbah, Aliyu Kibiya, ya bayyanawa Freedom Rediyo cewa sukan shugabanni a idon jama'a ya sabawa koyarwan addinin Musulunci.
Yace:
"Duk da cewa muna kira ga kowa a gari suyi abinda ya dace, muna daukan matakai daban-daban akan lamura daban-daban."
"Ya sabawa dokar addinin Musulunci a hau mimbari ana sukan shugabanni. Akwai hanyoyin da za'a yiwa shugaba gyara ba tare sukarsa a idon jama'a ba."
Amma kwamanda janar na Hisbah, Haroun Ibn-Sina, ya bayyana gidan rediyon cewa har yara masu hannu da shuni suna kamawa.
Hukumar Hisbah ta sammaci yar wasar Kannywood, Ummah Shehu
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sammaci yar wasar kwaikwayo, Ummah Shehu, zuwa ofishinta.
Hisbah ta gayyaci Ummah ne kan zargin da tayi cewa ta san wasu jami'an Hisbah dake neman mata.
Umma Shehu, ta yi barazanar tona asirin jami’an hukumar Hisba ta jihar Kano wadanda ta yi zargin suna neme-nemen mata.
Umma ta bayyana haka ne cikin wani faifan Bidiyo da ya shahara a kafafen sada zumunta, inda take jimamin yadda 'yan Hisbah suka kame wata kawarta, Sadiya Haruna bisa laifin shirya bidiyon batsa.
Asali: Legit.ng