Mutum uku sun mutu yayin da miyagun Yan bindiga suka kai sabon hari jihar Kaduna

Mutum uku sun mutu yayin da miyagun Yan bindiga suka kai sabon hari jihar Kaduna

  • Wasu gungun yan bindiga sun kai sabon hari kauyukan dake yankin karamar hukumar Zangon Kataf, Kudancin Kaduna
  • Lamarin ya faru ne a kauyen Machun da kuma Manuka, inda akalla mutum uku suka mutu wasu suka jikkata
  • Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya yi Allah wadai da harin tare da jajantawa mutanen da ya shafa

Kaduna - Rahoto ya nuna an kashe aƙalla mutum uku, wasu dama sun jikkata a wasu jerin hari da yan bindiga suka kai yankin karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Channels tv ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne ranar Jumu'a a kauyukan Machun da Manuka bayan kashe mutum 5 a Zangon Kataf a farkon watan Agusta.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da kai hare-haren a wata sanar wa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun sheƙe rai 1, sun tasa keyar 7 kan ƙin biyan haraji

Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna
Mutum uku sun mutu yayin da miyagun Yan bindiga suka kai sabon hari jihar Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahoton ya bayyana cewa maharan sun mamaye kauyukan biyu, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, a wannan lokacin suka harbe mutum uku har lahira, wasu da dama suka jikkata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki jami'an yan sanda suka ɗauka?

Aruwan ya kara da cewa jami'an yan sanda sun samu rahoton abinda ke faruwa a Ƙauyen Machun ta wayar salula, inda suka gaggauta zuwa wurin.

Aruwan yace:

"Yan sanda na isa Kauyen Machun aka sake shaida musu ana jin karar harbin bindiga a kauyen dake makwaftaka wato Manuka."
"Maharan sun tsere kafin zuwan yan sanda yayin da aka gano gawarwakin mutum uku a kauyen."

Ya kuma kara da cewa maharan sun jikkata mutane da dama a kauyen Manuka kuma an gaggauta kai su asibiti domin kula da lafiya.

Rl-Rufa'i ya maida martani

A martaninsa, Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya yi Allah wadai da sabbin harin Zangon Kataf, kuma ya yi wa waɗanda suka mutu addu'a.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

Gwamnan ya roki jami'an tsaro su yi iyakar bakin kokari su kamo waɗanda suka kai waɗannan harin domin su girbi abinda suka shuka.

Sannan ya yi fatan samun lafiya cikin sauri ga mutanen da suka jikkata yayin harin, kamar yadda premium times ta ruwaito.

A wani labarin kuma shugaban PDP na ƙasa, Uche Secondus, ya bayyana cewa yana nan daram akan mukaminsa

A kokarin da yake na rike matsayinsa, Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya musanta rahoton cewa ya yi murabus.

Shugaban ya bayyana cewa labarin da ake yaɗawa cewa bai je taron NEC ba saboda ya sauka ba gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262