Zamfara: Ƴan bindiga sun sheƙe rai 1, sun tasa keyar 7 kan ƙin biyan haraji

Zamfara: Ƴan bindiga sun sheƙe rai 1, sun tasa keyar 7 kan ƙin biyan haraji

  • Miyagun 'yan bindiga a jihar Zamfara sun sheke mutum 1 tare da sace mutum 7 a kauyukan da suka ki biyan haraji
  • An gano cewa 'yan bindigan sun kallafa haraji kan jama'ar kauyukan Dadah, Tukurawa da Gandamasu dake Zurmi
  • An yi yajejeniyar biyan harajin inda kayukan da basu da kudin biya za su yi aiki a gonakin 'yan bindigan jihar

Zamfara - Miyagun 'yan bindiga sun sheke mutum 1 kuma sun tasa keyar mutum bakwai a kauyukan Dadah, Tukurawa da Gandamasu a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Premium Times ta ruwaito cewa, miyagun 'yan bindigan sun kai farmaki kauyukan a daren Alhamis sakamakon kin biyan haraji da mazauna kauyen suka yi wanda 'yan bindigan suka kallafa musu.

Zurmi tana daya daga cikin kananan hukumomi a jihar Zamfara da 'yan bindiga suka gallaba. Suna da iyakoki da karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Gwamnan Neja ya gana da daliban Tegina 91 bayan kwanaki 88 da sukayi hannun yan bindiga

Wasu daga cikin yankunan Zurmi na da alaka da dajin Rugu inda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

Zamfara: Ƴan bindiga sun sheƙe rai 1, sun tasa keyar 7 kan ƙin biyan haraji
Zamfara: Ƴan bindiga sun sheƙe rai 1, sun tasa keyar 7 kan ƙin biyan haraji. Hoto daga VOA
Asali: UGC

A harin daren Alhamis, wani shugaban matasa na yankin, Abdullahi Yusuf, ya ce an sheke mutum daya kuma an sace mutane 7 a kauyen Dadah.

Hudu daga cikin wadanda aka sace mata ne. Abinda muka gane shine, wasu daga cikin mazauna kauyen ba su biya harajin da 'yan bindiga suka dora musu ba, lamarin da yasa suka kai farmaki," ya kara da cewa.

Ya ce jama'ar Gidan Zago sun biya dubu dari takwas da aka saka musu yayin da jama'ar kauyen Tsakauna suka amince za su yi wa 'yan bindigan aiki a gonakinsu.

Yusuf ya ce 'yan bindigan sun sakawa jama'ar Takurawa harajin naira miliyan tara, naira miliyan biyu kan jama'ar Dadah da kuma naira miliyan biyu da rabi kan Gidan Shaho.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sabon harin Jihar Benue ya yi ajalin rayukan mutane 8

Ya kara da cewa, bayan tattaunawa da suka yi, mazauna kauyen sun amince da za su biya wannan kudin.

Jama'ar kauyen Kurunkudu da ke karamar hukumar Bakura sun biya 'yan bindigan naira dubu dari biyu a matsayin kudin haraji.

Hamza Muhammad, wani mazaunin Bakura, ya sanar da Premium Times cewa an biya kudin harajin bayan wata yarjejeniya da aka yi tsakanin yankunan da 'yan bindigan.

Har a yayin rubuta wannan rahoton, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ba a samu damar tattaunawa da shi ba kafin rubuta wannan rahoton.

'Yan ta'adda 27 sun sheka lahira bayan rikici ya barke tsakanin 'yan Boko Haram da ISWAP

A wani labari na daban, 'yan Boko Haram da mayakan ISWAP da dama sun rasa rayukansu bayan wani mummunan karon batta da ya auku tsakanin kungiyoyin guda biyu da ke arewacin Abadam a jihar Borno.

Daily Nigerian ta tattaro bayanai a kan yadda 'yan Boko Haram da dama suka rasa rayukansu bayan fusatattun mayakan ISWAP da ke wuraren Gusuriya a kauyen Dumbawa sun kai musu farmaki.

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

'Yan Boko Haram suna hanyar zuwa mika da makamansu ga MNJTF a daidai iyakar Nijar ranar Lahadi, 22 ga watan Augustan 2021 aka kai musu farmaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel