Fadar shugaban kasa ta yi barazanar hukunta jami'an da aka samu da cin amana

Fadar shugaban kasa ta yi barazanar hukunta jami'an da aka samu da cin amana

  • Tijjani Umar, sakataren din-din-din na Fadar Shugaban Kasa, ya ce za a hukunta duk wani ma’aikacin Fadar Shugaban Kasa da aka samu da cin amana
  • Umar ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta, a Aso Rock, yayin da yake kaddamar da sashin yaki da cin hanci da rashawa da bayyana gaskiya
  • A cewarsa, yakamata membobin kungiyar su zama jakadu nagari a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa

Aso Rock, Abuja - Hukumomin fadar shugaban kasa ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ya ci amana da kin sauke hakkokin da aka dora masa yayin gudanar da aikinsa.

The News ta ruwaito cewa sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasa, Tijjani Umar ne ya yi wannan gargadin yayin kaddamar da sashin yaki da cin hanci da rashawa na fadar gwamnatin, a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta a Abuja.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

Fadar shugaban kasa ta yi barazanar hukunta jami'an da aka samu da cin amana
An kafa sashin yaki da cin hanci da rashawa a fadar shugaban kasa Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ce ta kaddamar da sashin.

Jaridar Premium Times ta kuma ruwaito cewa Umar ya lura cewa tawagar sashin yaki da cin hanci da rashawa ba za su ci amanar da aka dora musu ba ko kuma su bari a fara misali da su ba.

Ya ce:

“Muna sa ran tawagar ta ACTU fadar Shugaban kasa da aka kaddamar a yau ba za ta ci amanarmu ba, in ba haka ba hakan zai tilasta mana fara yin misali da ku idan aka samu kuskure.
"Ina ganin daga nan muka fara daga yau. A namu bangaren, mahukuntan za mu yi jagoranci mai kyau. Muna daukar wannan alƙawarin a yau kuma muna riƙe kanmu ga ɗimbin ɗabi'a, don kada ACTU ta damu kanta game da kallon ɓangaren gudanarwa."

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

Abin da ake tsammani daga membobin sashin

Umar ya taya membobin sashin murna, yana mai cewa musamman an zabo su daga cikin ma'aikatan fadar Shugaban kasa bisa nagarta da kokarinsu baki daya wajen aiwatar da ayyukansu.

Ya kara da cewa yana sa ran za su taimaka wa cibiyar ta hanyar ci gaba da ba da shawarwari, bayar da rahoto da kuma inda ya zama dole, aiwatar da doka.

Da ya samu wakilcin Daraktan sashin nazari, Abbia Udofia, shugaban ICPC ya ce hukumar ce ta samar da ACTUs a ma'aikatu, sassan da hukumomi tare da hadin gwiwar ofishin Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya (OHCSF) a 2001.

Ya yi bayanin cewa ACTUs wani bangare ne na sa ido, ganowa da magance tangarda a cikin tsarin ayyukan cibiyoyin gwamnati.

A wani labari na daban, mai girma Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya yi watsi da ikirarin da gwamnatin tarayya ta yi na cewa ta aika masa da Naira biliyan shida.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro na ganawa a Aso Rock

Gwamnatin tarayya ta ce Ebonyi tana cikin jihohin da suka karbi kudi domin gina wurin kiwon dabbobi.

Da aka yi hira da shi a Channels TV, mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, yace jihar Ebonyi ta karbi kasonta na kudin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel