Kiwon dabbobi: Gwamna ya karyata fadar Shugaban kasa, yace ba a aiko masa da N6bn ba

Kiwon dabbobi: Gwamna ya karyata fadar Shugaban kasa, yace ba a aiko masa da N6bn ba

  • Gwamnatin Ebonyi ta ce ba ta goyon-bayan a ware fili domin ayi kiwon dabbobi
  • Gwamna David Umahi ya musanya kalaman da suka fito daga bakin Garba Shehu
  • Umahi yace bai nemi gwamnatin tarayya ta ba shi kudi ba, kuma ba zai nema ba

Ebonyi – Mai girma Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya yi watsi da ikirarin da gwamnatin tarayya ta yi na cewa ta aika masa da Naira biliyan shida.

Gwamnatin tarayya ta ce Ebonyi tana cikin jihohin da suka karbi kudi domin gina wurin kiwon dabbobi.

Da aka yi hira da shi a Channels TV, mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, yace jihar Ebonyi ta karbi kasonta na kudin.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Gwamna David Umahi ya na tabbatar da cewa ba ya goyon bayan jihohi su ware wasu filaye domin dabbobi su iya yin kiwo.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

A wani jawabi da David Umahi ya fitar a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta, 2021, yace jihar Ebonyi ba ta da wani wurin da za ta iya ware wa makiyaya.

Jawabin gwamnan ya fito ta bakin mai ba shi shawara na musamman wajen yada labarai, Francis Nwaze.

Gwamna Umahi
Umahi ya hadu da Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

“Mun samu labarin da ke zagaya wa cewa jihar Ebonyi ta na cikin jihohin tarayyar da aka ba Naira biliyan shida domin a samar da wurin kiwon dabbobi.”
“Ana alakanta wannan magana da hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, lokacin da yake amsa tambayoyi a tashar Channels TV a daren Laraba.”
“Gwamnatin Ebonyi ba ta taba neman kudi domin gina wuraren yin kiwon dabbobi ba, kuma ba za ta taba neman kudin da wannan manufar a jihar ba.”

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya koka, masu rike da madafan iko sun haramta masa ganin Shugaba Buhari

Sanarwar ta kuma ce duk mai neman ya yi kiwon dabbobi a Ebonyi, ya yi wannan dawainiya da kansa cikin filinsa domin gwamnati ba ta da filin da za ta bada.

SEFORPILDF da ILDF sun yi magana a kan 2023

A jiya ne rahoto ya zo mana kungiyoyi irinsu Southeast for President and Igbo Leadership Development sun ce dole a ba ‘Dan kudu maso gabas takara a 2023.

Kamar yadda suka shaida wa manema labarai, kungoyoyin na Ibo za su yi shari’a da jam’iyyun siyasan kasar nan idan aka hana Inyamuri tikitin zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel