Da dumi-dumi: Shugaba Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro na ganawa a Aso Rock

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro na ganawa a Aso Rock

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osibanjo suna cikin ganawa da shugabannin tsaro
  • Suna ganawar ne a yau Alhamis, 19 ga watan Agusta a fadar Shugaban kasa da ke Abuja
  • Ana sa ran za a sanar da shugaban kasar batun halin da ake ciki a yaki da ake da ta'addanci a kasar

Abuja - A yanzu haka, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin ganawa da manyan hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa dake Abuja, jaridar Punch da PM News suka ruwaito.

Har ila yau a wurin taron akwai Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro na ganawa a Aso Rock
Shugaba Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro na ganawa a fadar shugaban kasa Hoto: Punch
Asali: UGC

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, ya bayyana cewa a ganawar za a sanar da Shugaban kasar ci gaban da aka samu a yaki da ta'addanci a kasar.

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Ana kuma sa ran ganawar za ta nuna nasarorin da sojoji suka samu a 'yan makonnin da suka gabata wadanda suka sa masu tayar da kayar baya da 'yan fashi da dama mika wuya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yaki da ta'addanci: Janar Irabor na neman taimakon hafsoshin soji da suka yi murabus

A wani labarin, mun ji cewa a ranar Laraba, Shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya, Janar Leo Irabor, ya ce sojoji suna bukatar samun dabaru da kwarin guiwa daga sojojin da suka yi murabus don cigaban kasa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya yi wannan furucin ne yayin jawabi a wani taron karawa juna sani na manyan sojojin Najeriya na yankin arewa ta tsakiya da suka yi a Makurdi.

A cewarsa, sojoji suna da damar da zasu kawo karshen duk wasu rashin tsaro da suke addabar kasa, amma ya bukaci sojoji masu murabus da kada su sare ko su yi tunanin sun fita daga cikin masu baiwa kasa tsaro, hasalima su amince da cewa suna da ruwa da tsaki a harkar tsaro.

Kara karanta wannan

Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona

Asali: Legit.ng

Online view pixel