Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun kutsa gidan sakataren NASIEC cikin dare sun sace shi

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun kutsa gidan sakataren NASIEC cikin dare sun sace shi

  • Yan bindiga sun yi awon gaba da sakataren Hukumar zaɓe mai zaman kanta na jihar Nasarawa
  • Rundunar yan sanda jihar ta bakin mai magana da yawunta Rahman Nansel ne ta sanar da hakan
  • Nansel ya ce korafin da aka shigar musu ya ce har gida ƴan bindigan suka bi sakataren suka sace shi

Lafia, Nasarawa - Ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace Mohammed Okpu, sakataren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Jihar Nasarawa, The Cable ta ruwaito.

Hakan na cikin wata sanarwar ne da mai magana da yawun yan sandan jihar Nasarawa, Rahman Nansel, ya fitar a ranar Laraba a Lafia.

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Sace Sakataren NASIEC a Nasarawa
Taswirar Jihar Nasarawa: Hoto: The Punch
Asali: UGC

The Cable ta ruwaito cewa Nansel ya ce kimanin yan bindiga biyar ne suka kutsa gidan sakataren na NASIEC a ƙauyen Bakin Rijiya da ke hanyar Lafia-Shendam misalin ƙarfe 11.45 na daren Talata.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sace Sakataren Hukumar Zaɓe a Jihar Nasarawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

"A ranar 26/08/2021 misalin ƙarfe 0145hrs, a shigar da korafi a C Division Lafia, cewa a ranar 24/08/2021 misalin ƙarfe 2345hrs, ƴan bindiga da ba a sansu kimanin 5 sun kutsa gidan sakataren NASIEC a ƙauyen Bakin Rijiya sun sace shi."

Matakin da Kwamishinan Yan sanda ya dauka?

A cewar kakakin, Adesina Soyemi, Kwamishinan yan sandan jihar ya jagoranci wata tawagar yan sanda daga sashin yaki da garkuwa, hana ta'addanci da wasu daban zuwa wani wurin da ake zargin yan bindigan na tsare da wanda aka sace.

Nansel ya ce yan sandan na bin sahun masu garkuwar kuma suna aiki domin ganin sun ceto shi.

Ya bukaci al'umma su rika taimakawa rundunar da bayyana masu amfani da za su taimaka a kama ɓata garin.

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

Kara karanta wannan

Harin yan bindiga kan makarantar sojoji abun kunya ne – Kungiyar ACF

A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel