'Yan Bindiga Sun Tare Motar Kuɗi, Sunyi Awon Gaba Da Muƙuden Kuɗaɗe Bayan Kashe Ɗan Sanda Da Direban Motar

'Yan Bindiga Sun Tare Motar Kuɗi, Sunyi Awon Gaba Da Muƙuden Kuɗaɗe Bayan Kashe Ɗan Sanda Da Direban Motar

  • Wasu ƴan fashi sun kai wa motar ɗaukan kuɗi hari a garin Ore, ƙaramar hukumar Odigbo a jihar Ondo
  • Rundunar yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da harin tare da mutuwar direban motar da ɗan sanda ɗaya
  • Ƴan sandan sun ce sun kaddamar da bincike don gano ɓata garin da suka tafka wannan ɓarnar

Rundunar ƴan sanda a jihar Ondo ta tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun kai wa motar ɗaukan kuɗi hari a Ore, The Guardian ta ruwaito.

Ƴan sanda sun kuma tabbatar da kashe direban motar da ɗan sanda ɗaya yayin harin.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito cewa harin ya faru ne a ranar Laraba da yamma a garin Ore, ƙaramar hukumar Odigbo na jihar.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun kutsa gidan sakataren NASIEC cikin dare sun sace shi

'Yan Bindiga Sun Tare Motar Kuɗi, Sunyi Awon Gaba Da Muƙuden Kuɗaɗe Bayan Kashe Ɗan Sanda Da Direban Motar
Motar Daukan Kudade. Hoto: Guardian NG
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NAN ta bayyana cewa wannan harin na zuwa ne kimanin makonni biyu bayan harin da aka kai wa motar kuɗin a Emure-Ile a jihar.

A cewar wani shaidan gani da ido:

"Ƴan fashin sun buɗe wa motar kuɗin ne da ke ɗauke da wani adadin kudi da ba a bayyana iyakarsa ba da motar ƴan sanda da ke bashi tsaro.
"An kashe direban motar da ɗan sanda yayin harin sannan an sace wani adadin kudi da ba a bayyana ba bayan harin."

Da ta ke tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar, DSP Funmilayo Odunlami, ta ce yan sanda suna kan neman maharan, The Guardian ta ruwaito.

'Yan sanda sun bazama neman maharan

Ta ce an fara bincike kan lamarin, tana mai kira ga mutanen garin su taimaka wa rundunar da bayanai masu amfani da zai taimaka a kama maharan.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibar Wata Jami'a, Sun Nemi a Tattaro Miliyoyi Kudin Fansa

"Eh, zan iya tabbatar maka cewa direban motar ɗaukan kuɗin da ɗan sanda sun mutu a harin, amma yan sanda sun fara bincike kan lamarin."
"Muna kira ga mutane da ke da wani bayani mai amfani su taimaka mana, ba mu buƙatar su bayyana sunan su amma su bada bayanai masu amfani da zai taimaka a kama maharan."

Ta kuma kara da cewa tuni an kai gawar waɗanda suka mutun zuwa asibiti.

NAN ta ruwaito cewa wannan harin shine na uku a cikin mako shida, a ƙalla yan sanda hudu aka kashe yayin harin.

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

An kama mutane 10 da suke da alaka da kai sabon hari kauyen Yelwa Zangam na Jos ta arewa da ke jihar Filato, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Gwamna Simon Lalong ya kwatanta harin a matsayin rashin imani, sannan ya shirya taro na gaggawa don tattaunawa da kuma neman hanyar kawo garanbawul ga kashe-kashen da aka maimaita a jiharsa.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Daliban Makarantar Bethel Baptist Kaduna

A wata takarda wacce darektan watsa labarai ya saki, Makut Mechan, ya ce gwamnan ya umarci jami’an tsaro su binciko duk wadanda suke da hannu a lamarin da masu daukar nauyinsu don a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164