Hukumar kwastam ta mika gurbattun magunguna na miliyoyi da ta kwata ga NAFDAC

Hukumar kwastam ta mika gurbattun magunguna na miliyoyi da ta kwata ga NAFDAC

  • Hukumar kwastam a jihar Kaduna ta mika wasu magunguna da ta kwace marasa rajista
  • Hukumar NAFDAC ce ta karbi kayayyakin da hukumar ta ta kwace a cikin watan Agusta
  • Hukumar NAFDAC ta bayyana karin hadin gwiwa da hukumar kwastam a irin wanna kokarin

Kaduna - Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta, ta karbi kayayyakin magunguna marasa rajista da darajarsu ta kai Naira miliyan 100 da Hukumar Kwastan ta kama.

Kwanturola a sashin B na sashin ayyukan kwastam na tarayya, Al-Bashir Hamisu ne ya mika kayayyakin ga NAFDAC a Kaduna, Daily Nigerian ta ruwaito.

Hukumar kwastam ta mika gurbattun magunguna na miliyoyi da ta kwata ga NAFDAC
Jami'an hukumar kwastam | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mista Hamisu ya ce rukunin masu sintiri na kan iyakokin kwastam sun kwace kayayyakin magungunan ne a watan Agusta.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Hukumar NCFRMI Ta Mika Kyauta Ga Gwamnan da Ya Fi Kowane Jin Kai da Tausayin Talakawa

“Kayayyakin yanzu suna hannun amintattu, kuma ina farin ciki saboda muna aiki mai kyau kuma ana ba da magungunan ga hukumar da ta dace don karin kulawar doka.
“Idan magungunan sun tafi inda bai dace ba, zai shafe mu kai tsaye ko a kaikaice.
"Na yi imani da hukumar saboda mutuncin su wajen tunkarar yanayi irin wannan."

Sai dai ya ce rundunar za ta ci gaba da tuntubar NAFDAC "saboda mutanen da ke bayan magungunan za su iya bullowa a ofishin NAFDAC".

Da yake mayar da martani, Kodinetan NAFDAC na Jihar Kaduna, Nasiru Mato, ya nuna godiya ga Hukumar Kwastam kan wannan babban kamun.

A cewarsa:

“NAFDAC tana da kyakkyawar alakar aiki da Kwastam kuma muna farin cikin karban magungunan; saboda wannan hadin gwiwar ne muke samun wannan babban sakamako.

Mato ya ce hukumar na fatan kara hadin gwiwa don samun babban sakamako.

Ya ce kayayyakin da aka samu sun hada da sirinji, Sildenafil citrate mai dauke da maganin kara kuzari na allura.

Kara karanta wannan

EFCC ta ba bankuna umarnin zakulo hanyoyin samun kudin shiga na 'yan Najeriya

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama kunshin tabar wiwi 404 da darajarsu ta kai miliyan 32 a jihar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kuma kwace wasu haramtattun kayayyaki da darajarsu ta kai Naira miliyan 234 daga shiyyar a zango na biyu na shekarar 2021.

Da yake nuna abubuwan a Sakkwato da Kebbi bi da bi a ranar Laraba, Mataimakin Kwanturola Olurukoba Oseni Aliyu, ya ce sauran kayayyakin da aka kwace sun hada da, shinkafa, jarakunan man fetur, katan din taliya da daurina yadi.

NDLEA Ta Kwamushe Wata Mata da Hodar Iblis 100 Kunshe Cikin Al'aurarta

A wani labarin, Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wata 'yar Najeriya da ke zaune a kasar Brazil, Misis Anita Ugochinyere Ogbonna, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe (NAIA) dake Abuja, dauke da kwalayen hodar iblis 100 da ta boye a al'aurarta da jakarta.

Kara karanta wannan

Rusau: Gwamnatin Kaduna ta ruguje manyan gine-gine a Barnawa da Narayi

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fada a ranar Lahadi a Abuja cewa an kama matar mai 'ya'ya uku ne a daren Juma’a lokacin da suka isa Abuja ta jirgin Qatar Air daga Sao Paulo na Brazil ta Doha babban birnin kasar Qatar.

A cewarsa, yayin binciken kwakwaf, an ciro hodar iblis 12 da ta saka a al'aurarta yayin da aka gano wasu kunshi 88 da aka saka a cikin safa a boye cikin jakarta, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.