EFCC ta ba bankuna umarnin zakulo hanyoyin samun kudin shiga na 'yan Najeriya
- Hukumar EFCC ta bukaci bankuna da su lura sosai kafin bude wa mutane asusun banki
- EFCC ta kuma bukace su da su tantance hanyoyin samun kudin abokan cinikayyarsu
- A cewar EFCC, wannan zai magance matsalolin da ake fuskanta na satar kudade a kasar
Abuja - Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bukaci bankunan kasar nan da su binciki hanyoyin samun kudin shiga na abokan cinikayyarsu kafin su bude musu asusu, The Guardian ta ruwaito.
Bawa ya ba da shawarar ne a ranar Talata 24 ga watan Agusta lokacin da Kungiyar Manyan Masu Binciken Bankunan Najeriya (ACAEBIN), karkashin jagorancin Shugabanta, Yinka Tiamiyu suka kai masa ziyarar ban girma a hedikwatar Hukumar dake Abuja.
EFCC ta roki ACAEBIN da su dauki batun nuna gaskiya a ayyukan banki da muhimmanci.
Ta kuma kara da cewa daga ranar 1 ga Satumba, 2021 ba za ta sake dagawa bankuna kafa ba kamar yadda ta saba domin hukumar za ta daura alhaki kan bankuna inda aka samu wasu laifuka na zamba ta bangarensu
Haka nan, ya tabbatar da shirye-shiryen hukumar na hadin gwiwa tare da kungiyar don magance laifukan da suka shafi kudi da kalubalen da ke da alaka a bangaren banki.
Daga cikin jawaban Bawa, ya ce:
"Ina rokun ku da ku san abokan cinikayyarku, ku san irin kasuwancin da suke yi kafin bude musu asusu saboda wasu abokan cinikayya za su iya bude asusu a tsakanin wata biyu kuma su zuba dimbin kudi a cikin asusun.
"Don haka akwai bukatar ku bincika da kuma tambayar wadannan bayanan ciki har da asusun da ke da alaka dasu."
Martanin kungiyar binciken bankuna ta ACAEBIN
Tiamiyu a cikin jawabinsa, ya ce ya kasance daga aikin ACAEBIN samar da ingantaccen hadin gwiwa tsakanin bankuna da EFCC wajen magance laifukan da suka shafi tattalin arziki da na kudi.
Ya sake nanata kudirin bankuna a matsayinsu na jagororin masu ruwa da tsaki a tsarin hada-hadar kudi na kasar don tsabtace tsarin, tare da lura da cewa ba manufar kungiyoyin ba ne kullawa ko murkushe munanan kudade.
Da yake karin haske kan wannan batu, Uduak Udoh, Mataimakin Shugaban Kungiyar ya ce:
“Wasu abokan cinikayyar suna hada kai da ma’aikatan banki don satar kudade.
"Muna son ku duba wannan bangare, ba bankunan kawai ba saboda a shirye muke mu ba ku duk hadin kan da kuke bukata; muna son ku aminta da masu binciken banki wajen musayar bayanai saboda ba za mu iya tallafa wa ma’aikatan 'yan damfara ba saboda barazana ne ga kungiyar.”
Sun yi amfani da damar ziyarar don zayyana abubuwan da ke damun su da kungiyoyin su, gami da bin diddigin koke-koke daga bankuna da EFCC ta yi.
Abdulrasheed Bawa: EFCC ta lissafa nasarorin sabon shugabanta bayan kwanaki 100 a ofis
A baya Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta lissafa nasarorin da shugabanta, Abdulrasheed Bawa ya samu, domin murnar cikarsa kwanaki 100 a kan mulki.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Bawa a watan Fabrairu domin ya shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawa bayan ficewar Ibrahim Magu.
Ga jerin nasarorin da Bawa ya samu a cewar EFCC:
1. An kwato N6,142,645,673.38 (sama da Naira biliyan 6), $ 8,236,668.75, £ 13,408.00, da € 1,730.00, dalar Kanada 200, CFA374,000.00, ¥ 8,430.00 (Yen na kasar Japan)
2. An kwato motoci 25, jirgin ruwa guda biyar, babura biyu, shago daya, filaye shida, kafet daya, kayan lantarki 13, kadarori 30, masana'anta daya, gidan mai guda daya.
3. An kwato manyan kayayyakin man fetur
4. An tabbatar da hukunci 185 daga kararraki 367 da aka shigar a fadin ofisoshin shiyya
Gwamnatin Buhari ta fara kaddamar da shirin N-Power a karo na uku
A wani labarin, Gwamnatin tarayya a ranar Litinin 23 ga watan Agustan 2021 ta fara kaddamar da shirin N-Power rukunin C shashi na farko, The Nation ta ruwaito.
Ma'aikatar agaji da ayyukan jin kai ta kasa ta fara aikin yin rajista na rukuni na uku na masu cin gajiyar shirin a ranar 26 ga Yuni, 2020.
Ministar agaji da ayyukan jin kai, Sadiya Farouq ta ce sama da mutum miliyan shida suka nuna sha'awarsu ga cin gajiyar shirin.
Asali: Legit.ng