Rusau: Gwamnatin Kaduna ta ruguje manyan gine-gine a Barnawa da Narayi

Rusau: Gwamnatin Kaduna ta ruguje manyan gine-gine a Barnawa da Narayi

  • Hukumar tsarawa da raya birane na jihar Kaduna ta rushe wasu gidaje a Barnawa da Narayi
  • Rahoto ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta fadi dalilin da yasa gwamnati ta dauki matakin rushewar
  • An kuma bukaci mazauna da asu dinga ba da hadin kai wajen bin umarnin gwamnati wajen cimma manufofinta

Kaduna - Hukumar tsarawa da raya birane ta jihar Kaduna (KASUPDA), ta rushe gine-gine guda tara masu tsada a Barnawa da Narayi saboda saba dokokin tsare-tsaren birane.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin KASUPDA, Nuhu Garba ya fitar a Kaduna, Daily Nigerian ta ruwaito.

Hukumar ta ce rusawar ta biyo bayan karewar wa'adin sanarwar da aka bayar ga masu gidajen da abin ya shafa.

Rusau: Gwamnatin Kaduna ta ruguje manyan gine-gine a Barnawa da Narayi
Rusasshen gida | Hoto: thisnigeria.com
Asali: UGC

Malam Nuhu Garba ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

”Rugujewar da aka yi a unguwar Barnawa ya faru ne saboda canjin akala da takura hanya.
"Tsarin da yake a fili mai lamba 44, Uganda Street a unguwar Barnawa, an cire shi saboda rashin samun amincewa da kuma canjin akala."

Barazana ga tsaro yasa aka rushe gidajen

Hukumar ta kuma ce an kawar da kuma ruguje gine-ginen ne saboda barazanar tsaro a kan titin Uganda dake a Barnawa.

Hukumar ta jaddada bukatar al'ummomi da sauran mazauna yankin su hada kai da shirin Sabunta Birane na Gwamnatin Jihar, kamar yadda News Diary ta tattaro.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa a ranar 1 ga Agusta, gwamnatin jihar ta ba da karin kwanaki biyar ga masu gidajen kan cewa su yi aiki da umarnin farko da aka ba su.

Garin Dadi: Kasar turai, inda za ka iya sayen katafaren gida a kasa da N500

A wani labarin, Legit ta tattaro muku labari mai kamar almara, yayin da bincike ya bankado cewa, akwai wani gari a kasar Italiya, inda mutum zai iya mallakar gida da karamin kudin da bai haura £1 wanda yake kwatankwacin N483.28 na Najeriya.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

Yanzu haka a garin mai suna Maenza ana siyar da tsoffin gidaje kuma an ba da rahoton cewa karin iyalai na tururuwan fitowa don sayar da tsoffin gidajensu.

Mutane da dama za su ga wannan batu ba komai bane illa zamba, duk da haka, an nakalto magajin garin Claudio Sperduti a kafafen yada labarai daban-daban da ke tabbatar da yarjejeniyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel