Ayade Ya Lashe Kyautar Gwamnan da Yafi Jin Kai da Tausayin Talakawa a Najeriya

Ayade Ya Lashe Kyautar Gwamnan da Yafi Jin Kai da Tausayin Talakawa a Najeriya

  • Hukumar NCFRMI ta mika kyautar gwamnan da ya fi ayyukan jin kai ga gwamnan Cross River, Ben Ayade
  • Hukumar tace ayyukan Ayade na tallafawa yan gudun hijira, baki da marasa galihu ya mamaye Africa
  • Gwamnan ya gode wa hukumar bisa wannan kyauta da ta tsamo shi ta bashi

Abuja - Hukumar kula da yan gudun hijira ta ƙasa (NCFRMI) ta bayyana gwamnan Cross River, Ben Ayade, a matsayin gwamnan da yafi aikin jin kai da agaji, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kwamishinan NCFRMI ta kasa, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ita ce ta bayyana haka a Abuja, yayin da take mika kyauta ga Gwamnan.

Tace agaji da taimakon da gwamna Ayade yake ga yan gudun hijira, baki da waɗanda aka raba mahallansu ya mamaye nahiyar Africa baki ɗaya, NCFRMI na alfahari da nasarorin gwamnan.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Gana da Shugaba Buhari Kan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai a Jos, Za'a Dau Mataki

Gwamna Ben Ayade Yayin amsar kyauta
Ayade Ya Lashe Kyautar Gwamnan da Yafi Jin Kai da Tausayin Talakawa a Najeriya Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Kwamishinan tace:

"Sadukarwar Ayade da nuna damuwarsa ga mutanen da wata kaddara ta afka mawa a bayyane yake kuma ya cancanci a yi koyi da shi."
"Mun gano cewa gwamnan ya jima ya na tallafawa yan gudun hijira, baƙi da ma waɗanda wani abu mara daɗi ya raba da mahallansu a Cross River."
"Bayan gano ayyuakn alherin da yake ga rukunin mutane daban- daban; karfin guiwa ga mutanen da suka cire tsammani, samar da matsugunai ga waɗanda suka rasa gidajensu, abinci ga mutanen dake jin yunwa."
"Saboda haka muka ga ya dace mu baiwa Gwamna Ayade kyautar ban girma domin kara masa karfin guiwa ya cigaba da irin waɗannan ayyukan jin kai da ya saba."

Aikin jin kai kamar addini ne a wajena- Ayade

Da yake nuna farin cikinsa, Gwamna Ayade ya gode wa hukumar bisa wannan kyauta da suka ba shi saboda cancantarsa.

Kara karanta wannan

Bayan Daukar Alkawari, Fulani Sun Tsamo Masu Garkuwa Daga Cikinsu Sun Mikawa Yan Sanda

Yace:

"Ayyukan jin kai da tallafawa marasa galihu kamar addini yake a wurina, kuma zan cigaba da yin iyakar bakim kokari na."

Ya bayyana hukumar NCFRMI a matsayin abokiyar aikin da ake bukata domin aiwatar da kudirin gwamnatin jihar na tallafawa marasa galihu.

A wani labarin kuma Baku San Abinda Kuke Yi Ba, Tsohon Sarkin Ƙano Sanusi II Ya Yi Magana Kan Raba Najeriya

Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, yace baya goyon bayan masu fafutukar a raba Najeriya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A cewar Sanusi, Khalifan Tijjaniyya a Najeriya, duk masu fafutukar ballaewa daga Najeriya ba su san abinda suke aikatawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel