Da Duminsa: Boko Haram sun shiga tasku, sojojin Najeriya sun hada kai da na Rasha

Da Duminsa: Boko Haram sun shiga tasku, sojojin Najeriya sun hada kai da na Rasha

  • Gwamnatin Najeriya ta sake rattaba hannu da kasar Rasha ta fannin sojoji da fasaha
  • Wannan na zuwa ne bayan karewar wa'adin yarjejeniyar ta shekaru da suka gabata
  • Legit ta tattaro manufar wannan yarjejeniya da gwamnatin Najeriya ta kullo da Rasha

Russia - Gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta fasaha da soji tare da tarayyar Rasha.

Wata sanarwa da rundunar sojin ruwan Najeriya ta fitar a ranar Laraba, 25 ga watan Agusta na nuna cewa ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (Rtd), wanda ke kan ziyarar aiki a kasar Rasha, ya sanya hannu a madadin Najeriya.

Legit.ng ta tattaro cewa daraktan ma’aikatan tarayya na hadin gwiwar soji da fasaha, Dmitry Shugaev, ya rattaba hannu a madadin tarayyar Rasha.

Kara karanta wannan

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Da Duminsa: Boko Haram sun shiga tasku, sojojin Najeriya sun hada kai da na kasar waje
Hotunan wajen rattaba hannu | Hoto: Nigerian Navy
Asali: Facebook

Jawabin sanya hannun wanda ya gudana a ranar Litinin, ya samu shaidar jakadan Najeriya a Rasha, Farfesa Abdullahi Y. Shehu, Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Auwal Zubairu Gambo, da sauran kusoshin tsaro.

Sauran wadanda suka halarci taron sune wakilan Sojojin Najeriya da Sojojin Sama na Najeriya, wasu manyan hafsoshin soji, da jami’an ma’aikatar tsaron Najeriya.

An tattaro cewa sabuwar yarjejeniyar ta kawo karshen yarjejeniyar farko da kasashen biyu suka kulla wadda aka kulla a ranar 6 ga Maris, 2001.

A cikin takaitaccen bayani bayan rattaba hannu, Ambasada Shehu ya nuna godiya ga mahukuntan Rasha kuma ya nanata cewa Najeriya ba ta neman komai a hadin gwiwar dace dacewa da fa'idodin juna.

Manufar yarjejeniyar

Legit.ng ta tattaro cewa yarjejeniya kan hadin gwiwar soji da fasaha tsakanin kasashen biyu yana ba da tsarin doka na samar da kayan aikin soji, ba da sabis bayan sayen makamai, horar da ma'aikata a cibiyoyin ilimi daban-daban da canja wurin fasaha, da sauran su.

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Jihar Zamfara ta samu sabon Shugaban Ma'aikata

Rattaba hannu kan yarjejeniyar wani babban ci gaba ne a alakar da ke tsakanin Najeriya da Rasha.

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce harin baya-bayan nan da aka kai Cibiyar Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA) a Kaduna zai taimaka wajen kara azama, kaimi da sa karfin soji wajen kawo karshen tashin hankali a kasar. Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa:

"Wannan mummunan aikin zai hanzarta kawar da munanan abubuwan da ke faruwa, wanda membobin rundunar sojin suka kuduri aniyar aiwatarwa cikin kankanin lokaci."

A cikin wata sanarwa da daya daga cikin masu taimaka masa a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya ce, shugaban ya lura cewa mugun nufin da masu aikata laifuka ke yi don rage martabar sojojin kasar a idon duniya ya gaza.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da sojoji ke ragargazar masu tayar da kayar baya, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran ire-iren masu aikata miyagun laifuka, musamman a arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

Rundunar soja ta karyata zarginta da ake da son maida tubabbun Boko Haram sojoji

A wani labarin, Rundunar Sojin Najeriya ta ce ba za ta dauki tsoffin 'yan ta'adda masu tayar da kayar baya a cikin rundunar sojojin Najeriya ba, The Cable ta ruwaito.

Kakakin rundunar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata 24 ga watan Agusta a babban birnin tarayya Abuja.

Nwachukwu ya ce hankalin sojoji ya je ga wani bidiyo da wani matashi ya watsa a kafafen sada zumunta kuma Anthony Jay ya shirya wanda ya danganta rugujewar sojojin Afghanistan da mika wuya ga mayakan Boko Haram a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel