Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

  • Hukumar makarantar NDA ta tabbatar da harin da 'yan bindiga suka kai mata a safiyar yau Talata
  • Kakakin NDA, Manjo Bashir Jajira ne ya tabbatar da lamarin inda ya sha alwashin cewa za su bi sawun maharan
  • Ya kuma tabbatar da kisan jami'ai biyu tare da sace daya

Makarantar horar da Sojin Najeriya (NDA) ta tabbatar da kisan jami’ai biyu a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari barikin a ranar Talata, 24 ga watan Agusta.

Sanarwar da jami'in hulda da jama'a na makarantar, Manjo Bashir Jajira ya fitar, ya ce 'yan bindigar sun sace wani jami'i, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda
Makarantar NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata sannan ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda Hoto: The Punch
Asali: UGC

NDA ta bayyana cewa tana kan bin diddigin 'yan fashin da suka yi kutse a tsarin tsaronta, jaridar Punch ta ruwaito.

Hadimin Shugaban kasa, Buhari Salau ya wallafa sanarwar kakakin rundunar a shafinsa na Facebook, inda yake cewa:

Kara karanta wannan

Jama’a sun ji hudubar Gwamnoni, sun tanadi bindigogi saboda gudun bacin rana

“Da safiyar yau wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi kutse a tsarin tsaro na Kwalejin sojojin Najeriya. A yayin wannan abin takaici, mun rasa jami’ai biyu kuma an sace daya.
“Makarantar tare da hadin gwiwar Babbar Runduna ta 1 ta Sojin Kasa da kuma Rundunar Horo ta Sojin Sama da sauran hukumomin tsaro da ke Jihar Kaduna na bin sawun masu garkuwar a yankin domin kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi.
“Kananan hafsoshi da ke samun horo da sauran al’umma da ke zaune a barikin NDA suna cikin aminci. Muna ba wa jama’a tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a cafke ’yan bindigar a kubutar da sojan.”

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA, sun hallaka Soja 2, sun sace 1

Kara karanta wannan

Majalisar Dinkin Duniya ta tono sirrin Gwamnatin Tarayya wajen kawo karshen yakin Boko Haram

A baya mun kawo cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kai mumunan hari makarantar horar da Sojin Najeriya NDA dake jihar Kaduna.

Rahoton ya nuna cewa yan bindigan sun hallaka mutum biyu yayinda suka yi awon gaba da jami'in Soja guda daya.

A riwayar Daily Trust kuwa, jami'in Sojan ruwa ne aka kashe yayinda mutum biyu da aka sace masu matsayin Manjo ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel