Da dumi-duminsa: Jihar Zamfara ta samu sabon Shugaban Ma'aikata
- Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya amince da nadin Alhaji Kabiru Muhammad Gayari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan jihar
- Hadimin gwamnan, Yusuf Idris Gusau ne ya tabbatar da nadin a yau Talata, 24 ga watan Agusta
- Nadin ya biyo bayan daukaka tsohon shugaban ma’aikata zuwa sakataren gwamnatin jihar
Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya amince da nadin Alhaji Kabiru Gayari a matsayin sabon shugaban ma’aikata na jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da darakta janar na yada labarai da wayar da kan jama’a da sadarwa na jihar, Alhaji Yusuf Idris ya fitar a Gusau ranar Talata, 24 ga watan Agusta.
Nadin ya biyo bayan daukaka tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Kabiru Balarabe zuwa sakataren gwamnatin jihar (SSG), jaridar Daily Post ta ruwaito.
A cewar sanarwar, nadin Kabiru Muhammad Gayari a matsayin Shugaban Ma'aikata ya fara aiki nan take.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ba da rahoton cewa Gayari, ya kasance Babban Sakatare na Ma’aikatar Kudi har zuwa lokacin da aka nada shi.
An dakatar da zaman majalisa a Zamfara saboda sace mahaifin kakakin majalisar
A wani labarin, majalisar Jihar Zamfara ta dakatar da zamanta har sai baba ta gani saboda sace mahaifin kakakin majalisar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Makonni uku da suka gabata ne yan bindiga suka sace mahaifin kakakin majalisar bayan kai hari a garinsu na Magarya a yankin Kanwa na karamar hukumar Zurmi.
Mahaifin kakakin majalisar da aka sace, Alhaji Mua'azu Abubakar shine hakimin Sabon Garon Magarya a yankin Kanwa a karamar hukumar.
Asali: Legit.ng