Kungiyar kare hakkin jama'a ta kai karar Buhari a kotu kan ‘bacewar’ Naira Biliyan 106 a 2018
- SERAP ta na karar gwamnatin Najeriya a babban kotun tarayya da ke Abuja
- Kungiyar ta bukaci a binciki wasu kudi da ake zargin sun bace daga ma’aikatu
- Za ayi shari’a da Shugaba Muhammadu Buhari, AGF da Ministar kudi a kotu
Abuja - Kungiyar nan ta 'Socio-Economic Rights and Accountability Project' wanda aka fi sani da SERAP, ta shigar da kara a kan gwamnatin Najeriya.
Socio-Economic Rights and Accountability Project ta kuma zuwa kotu
Legit.ng ta ji cewa wannan kungiya mai cin gashin kan-ta, ta maka gwamnatin Muhammadu Buhari a gaban wani babban kotun tarayya da ke Abuja.
SERAP ta bayyana wannan ne a shafinta na Facebook a ranar Asabar, 22 ga watan Agusta, 2021.
Kungiyar na zargin shugaba Muhammadu Buhari da kin hukunta wadanda suke da laifi a zargin bace war Naira biliyan 196 daga ma’aikatun gwamnati.
Kamar yadda muka ji, sauran wadanda za su amsa laifi a kotu sun hada da Ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami SAN.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka zalika ana karar Ministar tattalin arziki da tsare-tsaren kasafin kudi na kasa, Zainab Ahmed.

Asali: UGC
Wannan kungiya ta shigar da kara a kotu ne bayan zargin da ofishin mai binciken kudi na kasa ya yi na cewa N105,662,350,077.46 sun bace a shekarar 2018.
Ana zargin kudin sun yi batar-dabo ne daga ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya wadanda aka fi sani da MDAs 149 shekaru uku da suka wuce.
Me SERAP ta ke nema a kotu?
“A kara mai lamba FHC/ABJ/CS/903/2021 da aka shigar a kotun tarayya da ke Abuja a makon jiya, ana neman a tursasa wa shugaba Buhari ya binciki zargin bacewar N106bn.”
“(Buhari) ya tabbatar an hukunta duk wanda aka samu da laifi, kuma a dawo da kudin da aka dauka.”

Kara karanta wannan
FIRS na neman hanyoyin tatsar kudi, Twitter da sauran kamfanoni za su soma biyan haraji a 2022
“Dawo da wannan kudi zai taimaka wajen ganin gwamnatin tarayya ta rage adadin bashin da ta ke ci domin ta cike gibin da aka samu a kasafin kudin tattalin arziki.”
Kawo yanzu ba a sa ranar da Alkali zai fara sauraron wannan kara a babban kotun tarayyar ba.
Samuel Ortom ya na shirin zuwa kotu
Gwamna Samuel Ortom ya gargadi Gwamnatin Tarayya a kan yunkurin farfado da hanyoyin kiwon dabbobi, yace hakan ya ci karo da tsarin mulkin da ake kai a yau.
Samuel Ortom ya ce ba zai yiwu a wannan zamani, a dauki fili a ba dabbobi domin su yi kiwo ba. Tuni gwamnan ya ankarar da lauyoyinsa cewa su fara shirin tafiya kotu.
Asali: Legit.ng