Dalilin da yasa ba zamu iya kashe yan Boko Haram da suka mika wuya ba, Lai Mohammed
- Gwamnatin tarayya ta yi magana karon farko kan yadda zatayi da tubabbun yan Boko Haram
- Gwamnati tace bai kamata Najeriya ta kashe mutanen da suka tuba ba a idon duniya
- Lai Mohammed ya yi alkawarin cewa gwamnati ba zata bari wadannan mutane su cutar da jama'a ba
Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da zai hanata kashe tubabbun yan ta'addan Boko Haram.
Ministan Labaraida al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan a hirar da yayi da kamfanin dillancin labarai NAN ranar Juma'a, 20 ga Agusta, 2021.
Yace:
"Kawai ba za'a iya harbesu ba saboda akwai dokokin duniya da suka bada kariya ga fursunonin yaki.
"Abinda Sojoji ke yi shine idan suka mika wuya, suna daukan sunayensu domin tabbatar da cewa da gaske suke sannan a mayar da su cikin al'umma."
MURIC Ta Roƙi Jama’a Su Rungumi Tubabbun Ƴan Boko Haram
Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC tayi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar sojin Najeriya akan shiryawa da tubabbun mayakan Boko Haram da ISWAP.
MURIC ta bayar da wannan shawarar ne a wata takarda da ta saki a ranar Alhamis inda tace ya kamata a kula da tubabbun ‘yan ta’addan tamkar ‘yan uwa wadanda suka bata aka gansu.
A hukunta tubabbun yan Boko Haram kawai, Kungiyar Arewa Consultative Forum
Amma Kungiyar Arewa Consultative Forum, ta yi watsi da maganar yafewa yan ta'addan Boko Haram da suke mika wuya ga gwamnati da kuma sakinsu.
Shugaban kungiyar na kasa, Cif Audu Ogbeh, ya ce wajibi ne a hukunta yan ta'addan kan laifukan da suka aikata kan yan Najeriya.
Kungiyar Musulunci Ta MURIC Ta Roƙi Jama’a Su Rungumi Tubabbun Ƴan Boko Haram, a Kuma Koya Musu Sana’a
Ogbeh, wanda tsohon Ministan noma ne, ya bayyana hakan a jawabin da ya rattafa hannu kuma kakakin kungiyar, Emmanuel Yawe, ya sake a Kaduna ranar Talata.
Asali: Legit.ng