Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamna Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jos

Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamna Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jos

  • Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace sam ba zai lamurci duk wani yunkuri na tada zaune tsaye a jiharsa ba
  • Gwamnan ya faɗi haka ne bayan ya kai ziyarar duba wasu daga cikin waɗanda lamarin Jos ya shafa
  • Lalong yace lokaci ya yi da zai sa kafar wando ɗaya da duk wani dake kokarin dawo da hannun agogo baya a jiharsa

Plateau - Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace ba zai lamunci duk wani yunkuri na tada rikici a jiharsa ba ta hanyar yaɗa labaran ƙarya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Aƙalla matafiya 22 aka kashe a wani hari da aka kai kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta rewa, jihar Filato.

Harin, wanda aka kaiwa wasu jerin motocin Bas dake ɗauke da mabiya addinin musulunci dake kan hanyarsu ta komowa Ondo bayan halartar wa'azi a Bauchi, ya bar wasu mutum 14 cikin rauni.

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Yi Magana Kan Kashe Musulmai a Jos

Geamna jihar Filato, Simon Lalong
Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamna Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jos Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Lalong yakai ziyara ga mutanen da abun ya shafa

Da yake jawabi bayan ziyarar da yakai wa wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Lalong yace gwamnati zata cafke tare da hukunta kowaye ta samu da yaɗa labaran karya da ka iya tada wutar rikici.

Gwamna Lalong yace:

"Ba zamu bari a tada rikicin addinai ba, mutane su dakatar da yaɗa labaran da basu da asali, irin wannan kisan na faruwa ne ta sanadiyyar haka."
"Ina tabbatar muku zamu sa kafar wando ɗaya da mutanen dake yaɗa sakonnin karya waɗanda ke jawo ana hallaka mutanen da ba su ji ba basu gani ba."
"Wannan gargaɗi ne kai tsaye ga duk wanda keson dawo mana da abinda muka mance da shi. Lokaci ya yi da zamu ɗauki mataki kan waɗannan mutanen duk mukaminsu."

Kara karanta wannan

Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga

Gwamnan ya kara da cewa ya kai wannan ziyarar ne domin duba yadda mutane ke ɗa'a ga dokar zaman gida da gwamnatinsa ta sa a yankin.

Zuwa yanzin rundunar sojin Operation Safe Haven ta kame mutum 12 da ake zargin suna da hannu a kisan.

A wani labarin na daban kuma Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Jihar Kaduna

Aƙalla mutum uku suka rasa ransu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai kauyen Gora Gida, karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Da yake magana da dailytrust, Hakimin Gora, Mr Elias Gora, yace yan bindiga sun kai harin ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi.

Ya kara da cewa wata mata ta samu raunin harbin bindiga sannan kuma maharan sun kona mota guda ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel