An Sake Kashe Mutum 7 Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai a Jos

An Sake Kashe Mutum 7 Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai a Jos

  • An sake gano gawarwakin wasu mutum 7 biyo bayan kisan gillan da aka yiwa musulmai a Jos
  • Rundunar yan sandan Filato na tsammanin wannan kisan na da alaƙa da na farko da aka yi ranar Asabar
  • Kwamishinan yan sanda da sauran shugabannin hukumomin tsaro na jihar sun gana da gwamna da daren Lahadi

Plateau - An sake kashe mutun 7 ranar Lahadi a yankin karamar hukumar Jos ta arewa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Hukumar yan sanda na ganin wannan kisan na biyu yana da alaƙa da kisan gillan da aka yi wa matafiya a kan hanyar Rukuba a Jos.

Kwamishinan yan sandan jihar Filato, Edward Ebuka, shine ya sanar da kashe mutanen a karo na biyu ranar Lahadi da daddare jim kaɗan bayan taron tsaro a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Ba ma son a kama sunan wani kan kisan musulmai a Jos, Kwamishinan 'yan sandan Filato

An sake kashe mutum 7 a Jos
An Sake Kashe Mutum 7 Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai a Jos Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mutum nawa aka ceto yanzun?

Yace gwamnatin jihar ta ɗauki matakin sanya dokar hana fita na tsawon awanni 24 a yankin ne domin dakile tayar da rikici.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar kwamishin, cikin wani jawabi da kakakin gwamnan Filato, Makut Simon Macham, ya fitar, an ceto adadin mutum 36 cikin koshin lafiya daga harin na ranar Asabar.

Ebuka ya kara da cewa:

"Waɗanda suka aikata kisan basu kaunar zaman lafiya, kuma suna son amfani da yanayin da ake ciki ne su tada zaune tsaye domin su samu damar yin sata."
"Wannan ba shine karo na farko da irin haka ta faru ba, bamu son kiran sunan kowa. Wasu bara gurbi ne kawai suke son amfani da wannan damar."

Wane mataki jami'an tsaro suke ɗauka?

Kwamishina Ebuka ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro baki ɗaya zasu fita binciko waɗannan yan ta'addan da bara gurbi domin su fuskanci hukunci.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Ya kuma yi kira ga al'ummar yankin da su yi biyayya da matakin gwamnati na zama a gida kuma su kauce wa duk wani rikici.

A cewarsa hukumomin tsaro zasu cigaba da zagayawa domin tabbatar da an bin umarnin gwamna na dawo da doka da oda.

Wane taro aka gudanar a gidan gwamnati

Shugabannin hukumomin tsaro sun yiwa gwamna Simon Lalong, bayani game da halin da ake ciki a lamarin tsaron jihar.

Hakanan sun bayyana masa halin da ake ciki wajen aiwatar da dokar hana fita na tsawon awa 24 a ƙananan hukumomin Jos ta arewa, Jos ta Kudu da kuma Bassa.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da kwamandan rundunar Operation Safe Haven, Kwamishinan yan sanda, kwamandan sojojin sama da kuma Daraktan DSS.

A wani labarin kuma Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamna Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jos

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace ba zai lamunci duk wani yunkuri na tada rikici a jiharsa ba ta hanyar yaɗa labaran ƙarya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Aƙalla matafiya 22 aka kashe a wani hari da aka kai kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta rewa, jihar Filato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel