Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

  • Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya umarci a kwamushe duk wanda yayi azarbabin zuwa belin wani daga cikin wadanda ake zargi da kashe-kashen Jos
  • Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Talata yayin taron gaggawa da ya shirya da jami’an tsaron jiharsa don samar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali
  • Kamar yadda rohotanni suka tabbatar, an yi taron gaggawar ne a ranar 14 ga watan Augusta akan farmakin da aka kai karamar hukumar Bassa, Jos ta kudu, Barkin Ladi da Riyom

Jos, Filato - Simon Lalong, gwamnan jihar Filato ya bayar da umarnin damke duk wanda yayi gaggawar zuwa belin wandanda aka kama ana zargin suna da hannu a kan farmakin jiharsa.

Gwamnan jihar ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron gaggawa da yayi da manyan jami’an tsaro a Jos, Thecable.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kisan Musulmai a Jos: Majalisar malamai ta ce kada Musulmai su dauki doka a hannu

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong
Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong. Hoo daga thecable.ng
Asali: UGC

Gwamna Yayi taro da jami'an tsaro

Kamar yadda NAN ta ruwaito, an yi taron na musamman ne a ranar 14 ga watan Augusta akan harin da aka kai karamar hukumar Bassa, Jos ta kudu, Barikin Ladi da Riyom.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar 14 ga watan Augusta, akalla mutane 22 aka kashe, yayin da mutane da dama suka samu miyagun raunika sakamakon harin da bata-gari suka kaiwa musulmai da suka dawo daga zikirin sabuwar shekarar musulunci suna kan titin Rukuba dake karamar hukumar Jos ta arewa.

Yayin da Lalong yake bayyana takaicinsa akan harin, ya tabbatar da cewa sai ya dauki mummunan mataki akan duk wanda aka kama da hannu a harin sannan zai tallafa wa wadanda suka cutu a dalilin harin.

Duk wanda yayi gaggawar zuwa belin a damke shi

Idan aka kama duk wadanda suka yi gaggawar zuwa belin wadanda ake zargi zai bankado hanyoyin da zasu kawo hanyar kawo maslaha a jihar Filato,” a cewarsa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Sake Kashe Mutum 7 a Jos Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai

Idan kun samesu ku kamasu. Ida wasu sukazo belin wani cikinsu, ku kwamushe su.”

A cewarsa hakan ne kadai zai hana mutane gangamin zuwa maganar belin wadanda ake zargin suna da hannu akan kashe-kashen da kuma wadanda suka dauki nauyin kashe-kashen.

Lalong ya yi taron da manyan mutanen jiharsa ciki har da tsofaffin gwamnoni, shugabannin ‘yan siyasa, shugabannin gargajiya da shugabannin anguwanni don jin ta bakinsu akan hanyar shawo kan rashin tsaro a Filato.

Kamar yadda Thecable.ng ta ruwaito, a cewar gwamnan, rashin tsaro a kananun hukumomi suna bukatar jajircewa da dagewa matukar anaso a kawo karshensu.

Ba zamu yi abinda zai kawo cikas ga yaranmu da jikokinmu ba,”a cewarsa.

Gwamnan ya bayyana damuwarsa akan yadda mutane suke kawo karairayi a kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da labarai da bidiyoyin karairayi.

Irin wadannan sakonni sune suke kara tayar da tarzoma. Kuma na umarci jami’an tsaro da su kama duk wanda suka kama yana yada karairayi kuma ya fuskanci fushin hukuma,”a cewarsa.

Kara karanta wannan

Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamnan Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jiharsa

Gwamnan ya ja kan mutane akan zanga-zanga inda yace hakan ba hanya mai bullewa bace.

Nasara daga Allah: Sojoji sun cafke hadimin gwamna dake daukar nauyin 'Unknown Gunmen' a Kudu

Rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar damko hadimin gwamna ne wanda yake kulle-kullen rura wutar ta’addanci a kudu maso gabas.

An bankado wanda ake zargin yana da hannu akan kaiwa mutanen gari da jami’an tsaro farmaki a kudu maso gabacin Najeriya.

PRNigeria ta tattaro bayanai akan yadda wani Tochukwu Okeke alias Owo, hadimin gwamna a kudu maso gabas ya daurewa ‘yan bindiga gindi kamar yadda rundunar division 82 na sojin Najeriya a Enugu suka bankado.

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel