'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

  • Rundunar 'yan sanda ta yi nasarar cafke wata budurwa dake hada kai da 'yan IPOB wajen barna
  • An gano ita ke karbo wa 'yan IPOB makamai da miyagun kwayoyi sannan da taya su kitsa barna
  • A halin yanzu tana hannun 'yan sanda, an kuma yi nasarar samun bayanai masu amfani daga gareta

Abuja - Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) tare da hadin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro sun cafke wata budurwa yar shekara 22 mai suna Gloria Okolie.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwar da mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Aremu Adeniran, ya fitar kuma Legit.ng Hausa ta samu a ranar Lahadi, 22 ga watan Agusta.

Adeniran ya lura cewa an kama Okolie ne saboda hada kai da ta yi a cikin jerin hare-haren da aka kai da gangan kan jami'an tsaro, wasu muhimman wurarenmallakin kasa ciki har da ofisoshin INEC da kashe jami'an tsaro a yankin kudu maso gabashin kasar.

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati
Dan sandan Najeriya | Hoto: ndtvimg.com
Asali: UGC

A cewarsa, wacce ake zargin 'yar asalin Umutanza ne a jihar Imo, an cafke ta ne bayan bincike da aiwatar da aikin na musamman na Operation Restore Peace, da sauran abubuwa.

Ya ce sauran laifukan da ake zargin Okolie dashi sun hada da ba da bayanai, kwayoyi da sarkar samar da makamai ga haramtacciyar kungiyar IPOB da reshen makamai, kungiyar ta'addanci ta ESN a yankin kudu maso gabas.

Sanarwar ta ce:

"Kamun nata da kuma bankadowa daga ikirarinta sun taimaka wa 'yan sanda wajen cafke "Onye Army ", babban ci gaba a kokarin dawo da doka da oda a yankin kudu maso gabas."

Ta yaya ta samu damar aikata wannan laifi?

Adeniran ya lura cewa karin binciken da rundunar 'yan sandan ta yi ya nuna cewa Gloria Okolie ta yi amfani da jinsinta na mace da kuma kamannin marasa laifi a wajen gudanar da ayyukan leken asiri kan sojoji da 'yan sanda a madadin IPOB/ESN.

Kara karanta wannan

Mutumin da ya yi shekara 41 yana shari’a da makarantarsa ya mutu bayan ya ci nasara

Ya bayyana cewa wacce ake tuhuma tana aiki a matsayin 'yar aike, wacce ke karban tsabar kudi, kwayoyi da makamai a madadin IPOB/ESN kuma tana kaiwa ga kwamandojin su a can sansanin su.

'Yan sandan sun kara da cewa ta hanyar ayyukanta na leken sirri, ta taimaka sosai wajen yawaitar aikata kisan kai, kone-kone da barna mai yawa ga dukiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati ta hanyar hada kai da ESN.

Ya ci gaba da cewa:

“Yawancin munanan hare-haren da aka kai wa jami’an tsaro da kadarori, tare da asarar rayuka masu yawa, suna da alaka da Gloria Okolie, 'yar leken asirin mayakan ESN. An kammala bincike don baiwa 'yan sanda damar gurfanar da ita a gaban kotu domin yi mata hukunci."

Batun kame Sunday Igboho: An ci taran ministan shari'a Malami N50,000 akan Igboho

A wani labarin, Wata Babbar Kotun Jihar Oyo da ke zama a Ibadan ta tsawaita umurnin da ta bayar na hana hukumar tsaro na farin kaya daga kame dan awaren Yarbawa, Sunday Igboho, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Mai shari'a Ladiran Akintola, wanda ya bayar da umurnin a ranar 4 ga watan Agusta a zaman da aka ci gaba da yi a ranar Laraba ya kuma ba da umarnin Malami ya biya N50,000 kasancewarsa wanda ake kara na farko.

An ba da umarnin biyan kudin daga Malami ne saboda shigar da martaninsa kan karar da Igboho ya shigar a kan lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel