Mutumin da ya yi shekara 41 yana shari’a da makarantarsa ya mutu bayan ya ci nasara

Mutumin da ya yi shekara 41 yana shari’a da makarantarsa ya mutu bayan ya ci nasara

  • Shugaban kungiyar NANS na farko a tarihi, Sunday Oladele, ya bar Duniya
  • Oladele ya mutu ne bayan shekara da shekaru ya na shari’a da YABATECH
  • Ubangiji ya karbi ran dattijon ne bayan an ce a dawo masa da satifiket dinsa

Oyo - Shugaban kungiyar daliban Najeriya na farko, Sunday Oladele, ya samu nasara a shari’ar da yake ta faman yi da kwalejin fasaha ta Yaba da ke garin Legas.

Jaridar Punch tace Sunday Oladele ya yi galaba bayan shekaru 41 ana ta shari’a tsakaninsa da makarantar a sakamakon karbe masa satifiket dinsa da aka yi.

Rahotanni suna zuwa daga bakin ‘dansa, Olalekan cewa ubangiji ya karbi ran mahaifinsa a ranar Talata.

Olalekan yace dattijon ya mutu a lokacin da yake murnar nasarar da ya samu a kan hukumomin Yabatech da majalisa ta ba umarni su maida masa satifiket dinsa.

Kara karanta wannan

Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona

Olalekan ya yi jawabi a ranar 17 ga watan Agusta, 2021, a Abuja lokacin da ‘yan kwamitin birne mahaifinsa, Marigayi Oladele suka yi magana da manema labarai.

Sanata Dino Melaye da shugaban kungiyar NANS, Sunday Asefon, suna nan aka yi maganar, suka kuma yi kira ga gwamnati tayi abin da ba za a manta da tsohon ba.

Yabatech
Makarantar Yabatech Legas Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya abin ya faru?

Jaridar ta ce Oladele da wasu abokan karatunsa suka haifar da kungiyar dalibai ta NANS a 1980 bayan gwamnatin Olusegun Obasanjo ta kashe kungiyar NUNS.

Zangar-zangar ‘Ali Must Go’ da shugaban NUNS na lokacin, Olusegun Okeowo, ya jagoranta ne ya sa gwamnatin sojan ta haramta wa dalibai kafa wata kungiya.

Daga baya, Sunday Oladele suka kafa kungiya mai suna NANS wanda ta yi karfi. A dalilin wannan aka karbe takardar shaidar karatunsa tun 1981, aka hana shi.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Sai bayan shekaru 41 da kuma sa bakin kwamitin Sanatoci, aka dawo wa Oladele satifiket dinsa, da niyyar sake gabatar masa a bikin yaye daliban bana da za ayi.

Makonni biyu da samun nasara, tsohon ‘dan gwagwarmayar ya rasu, an kafa kwamitin da zai birne shi.

Za a sayo karnukan N650m

An ji Najeriya za ta kashe Naira Miliyan 658 kan karnukan da suke tsare filayen jirgin sama domin gano masu yunkurin fito ko shigo wa da miyagun abubuwa.

Haka zalika an samu labari cewa Majalisar FEC ta amince da kwangilar gina filin jirgin sama a Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel