Batun kame Sunday Igboho: An ci taran ministan shari'a Malami N50,000 akan Igboho

Batun kame Sunday Igboho: An ci taran ministan shari'a Malami N50,000 akan Igboho

  • Babbar kotu mai zama a Ibadan ta ci tarar ministan shari'a Abubakar Malami tarar NN50,000
  • An bukaci Malami ya biya kudin ne ga lauyoyin Sunday Igboho bisa wasu dalilai da suka mika
  • Hakazalika, Malami ya bukaci kotun da ta janye batun hana DSS kame Sunday Igboho nan kusa

Oyo - Wata Babbar Kotun Jihar Oyo da ke zama a Ibadan ta tsawaita umurnin da ta bayar na hana hukumar tsaro na farin kaya daga kame dan awaren Yarbawa, Sunday Igboho, Punch ta ruwaito.

Mai shari'a Ladiran Akintola, wanda ya bayar da umurnin a ranar 4 ga watan Agusta a zaman da aka ci gaba da yi a ranar Laraba ya kuma ba da umarnin Malami ya biya N50,000 kasancewarsa wanda ake kara na farko.

Kara karanta wannan

'Batanci: Gwamnatin Kano Ta Ɗauki Manyan Lauyoyi 4 Masu Muƙamin SAN Don Shari'ar Abduljabbar

An ba da umarnin biyan kudin daga Malami ne saboda shigar da martaninsa kan karar da Igboho ya shigar a kan lokaci.

Batun kame Sunday Igboho: An ci taran ministan shari'a Malami N50,000 akan Igboho
Ministan Shari'a, Abubakar Malami SAN | Hoto: channelstv.com
Asali: Facebook

Igboho, wanda ya kara yawan lauyoyinsa tare da wasu kwararrun Lauyoyi biyu na Najeriya: Adekola Olawoye da Oladipo Olasope sun nemi Malami ya biya su N250,000 amma kotu ta ba da umarnin biyan N50,000.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A janye batun hana kame Sunday Igboho

Abubakar Malami, a gaban wata babbar kotun jihar Oyo ya nemi a janye umarnin hana kame Sunday Igboho, da daskare asusun bankinsa.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa a cigaba da sauraron karar a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, Abdullah Abubakar, lauyan da ke wakiltar AGF, ya sanar da kotun cewa ya shigar da korafi na farko kan lamarin.

Abubakar bai iya motsa bukatar tasa ba, tunda ya shigar batun a kan lokaci. A cewarsa, jinkirin ya faru ne saboda ba a yi masa bayani kan lamarin ba a lokacin da ya dace. Don haka, ya roki kotu da ta kara masa lokaci.

Kara karanta wannan

Abduljabbar ya rame: Sheikh Abduljabbar ya sake gurfana a gaban kuliya

Kotu ta yankewa barawon Al-kur'ani hukucin sharan masallaci na kwanaki 30 a Kano

A wani labarin, Wata kotun shari’a da ke zama a Fagge 'Yan-Alluna a Kano ranar Talata 17 ga watan Agusta ta umarci Halifa Abdullahi da ya share masallacin Juma’ar Fagge na tsawon kwanaki 30 a jere a matsayin hukuncinsa na satan kwafin Alkur’ani mai girma guda takwas.

Mista Abdullahi, mazaunin unguwar Yola da ke cikin birnin Kano, an zarge shi da sata a masallaci a unguwar Tudun Maliki ranar Lahadi da daddare tare da kwashe kwafin Alkur'ani guda takwas.

Sai dai jami'an tsaron masallacin sun cafke wanda ake zargin bayan ya aikata laifin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.