Masani: Malaman Najeriya za su iya gogayya da kowane irin malami a duniya

Masani: Malaman Najeriya za su iya gogayya da kowane irin malami a duniya

  • Malaman Najeriya za su iya kasancewa masu gogayya da duk wani malami a duniya in ji masani
  • Wani masani a fannin ilimi ya bayyana irin kokarin da ake wajen sauya tsarin karantarwa na malaman Najeriya
  • Masanin ya kuma bayyana cewa, malaman Najeriya sun samu damar sauyawa zuwa kwararrun malamai

Yayin da ake ci gaba da kokarin ganin an daukaka darajar aikin koyarwa, da alama akwai kyakkyawan fata ga kowane malamin makaranta a Najeriya.

A wata hira ta musamman da Legit.ng ta yi da Ebere Anyanwu, alkalin shirin TV na Naija Teacher's Reality ya bayyana cewa babban makasudin shirin shine samar da gogaggu kuma kwararrun malamai wadanda zasu yi tasiri kan ilimi ga yaran Najeriya.

Masani: Malaman Najeriya za su iya gogayya da kowane irin malami a duniya
Kwararren Malamin Makaranta, Ebere Anyanwu | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Babban matsayin kwarewa da ake sa rai daga malaman Najeriya

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Anyanwu, kwararre a fannin ilimi, ya ce yana sa ran wanda zai ci nasara a shirin zai kasance yana da kaifin basira, kwarewa, da fahimtar abin da aikin koyarwa da da'a ya kunsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Anyanwu ya kuma ce yana fatan wanda zai ci nasarar, wanda dole ya zama malami ne na karni na 21 ya kasance ya fahimci abin da ake bukata don yin gasa tare da sauran malamai a makarantun kasashen waje kuma mafi mahimmanci wajen isar da kowane aiki na koyarwa.

Ya lura cewa cikakken malami ya kamata ya zama kwararre ta yadda zai iya fahimtar bukatar kowane dalibi - wanda yake na musamman - kuma yana iya yin tasiri akan ilimi a kowane lokaci na rayuwar dalibi.

Ya ce a cikin shirin na talabijin da ake gudanarwa, an ba da dama ga kowane malamin Najeriya wajen fahimtar bukatar dalibi ko wuraren da ake bukatar habakawa a ilmance.

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Malaman sun kuma koyi yadda mafi kyawun aiki tare da al'ummarsu yake wajen tasirantuwar koyo ga dalibansu.

Anyanwu ya ce:

"Wasu daga cikin ayyukan da muke yi anan ayyuka ne da za su koya wa wadannan malaman sanin wuraren ingantawa kan dalibansu a cikin aji; mafi yawan wadannan lokutan abin da muke yi ayyuka ne na aji amma wani lokacin mukan fita wajen aji don nuna musu ainihin abin da ke faruwa a cikin aji yadda za su iya yin hakan da kyau."

Ya kuma bayyana cewa shirin, wanda aka fara a shekarar 2019 tun farko, ya samu nasarar canza rayuwar malaman Najeriya da yawa - ta kai tsaye ko a kaikaice - don samar da damarmaki da suka hada da ci gaba a aiki, kwarin gwiwar aiki, da manyan abubuwan rayuwa ga malamai.

Malamai a matsayin masu canjin rayuwa kuma abin kishin kowa

Anyanwu ya kara da cewa a karshe, yana sa ran shirin zai fito da damarmaki daban-daban ga kowane malamin Najeriya - wanda ya ke cikin tsangwaman koma baya - ya zama abin kishin kowa.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

Yace:

“Wasu daga cikin baiwarsu (malaman) da ba su taba sani ba an bayyana musu anan kuma a karshen, muna godiya ga Allah saboda da yawa daga cikin su sun samu kwarewa sosai.

Ya kuma bayyana cewa, masu ganin aikin koyarwa a matsayin koma-baya, yanzu ya kamata su fahimci abin ido bude, in da yake cewa:

"A karshe dai, mutane saboda alama da aka lika kan malamai na koma-baya, amma yanzu sun ga cewa aikin koyarwa na iya kawo musu wani abu mai kyau a rayuwa."

Kotu ta yankewa barawon Al-kur'ani hukucin sharan masallaci na kwanaki 30 a Kano

A wani labarin na daban, Wata kotun shari’a da ke zama a Fagge 'Yan-Alluna a Kano ranar Talata 17 ga watan Agusta ta umarci Halifa Abdullahi da ya share masallacin Juma’ar Fagge na tsawon kwanaki 30 a jere a matsayin hukuncinsa na satan kwafin Alkur’ani mai girma guda takwas.

Kara karanta wannan

Tsadar abinci: Dalilin da yasa 'yan Najeriya za su ci gaba da cin bakar wahala, in ji masana

Mista Abdullahi, mazaunin unguwar Yola da ke cikin birnin Kano, an zarge shi da sata a masallaci a unguwar Tudun Maliki ranar Lahadi da daddare tare da kwashe kwafin Alkur'ani guda takwas.

Sai dai jami'an tsaron masallacin sun cafke wanda ake zargin bayan ya aikata laifin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel