Gwanda aikin tukin Keke Napep da koyarwa: Malamar makaranta ta ajiye karantarwa
1 - tsawon mintuna
- Wata 'yar Imo ta bayyana yadda ta ajiye karantarwa ta fara tukin Keke Napep
- Budurwar tace kudin da take samu a harkar tuki ya ninka abinda take samu tana karantarwa a aji
- Yan Najeriya sun yi tsokaci kan bidiyonsa inda suka wasu suka yarda da maganarta
Bidiyon wata budurwa yar Najeriya a Imo tana tukin Keken 'a daidaita sahu' ya tayar da hankalin mutane a kafafen ra'ayi da sada zumunta.
A gajeren bidiyon da @Instablo9ja ta daura, budurwar ta ce ta karanci ilimin addini a jami'ar Calabar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Aikin karantarwa babu kudi
Yayinda aka tambayeta shin me dalilin da yasa ta fara wannan aiki na tuki, budurwar ta bayyana cewa kudin da take samu yanzu ya fi wanda take samu matsayin Malama.
Tace sai da ta karantar a makarantu masu zaman kansu kafin ta yanke shawarar ajiyes.
Tace ta gaji da yan sulalla da ake bata matsayin Malama.
Asali: Legit.ng