Gwamnan PDP: Mun yafe wa duk wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP

Gwamnan PDP: Mun yafe wa duk wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP

  • Gwamnan jihar Bayelsa ya magantu kan masu yawan sauya sheka daga PDP zuwa wata jam'iyyar
  • A cewarsa, PDP ta yafe musu, kuma kofa a bude take idan suna son dawowa jam'iyyar ta PDP
  • Ya kuma shaida cewa, jam'iyyar PDP za ta ci gaba da zawarcin wadanda suka sauya sheka ko za su dawo

Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya ce jam'iyyarsa ta PDP ta yafewa duk wadanda suka fice daga jam'iyyar kafin yanzu, ya kara da cewa har yanzu kofa a bude take ga wadanda suke son dawowa, New Telrgraph ta ruwaito.

Da yake magana a ranar Laraba 18 ga watan Agusta a Yenagoa yayin kaddamar da sabuwar sakateriyar jam'iyyar, gwamnan ya bayyana cewa tuni da yawa sun dawo kuma ya shawarci masoya jam'iyyar da su je su dawo da ragowar.

Read also

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

Gwamnan PDP: Mun yafe wa duk wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP
Gwamnan jihar Bayelsa | Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

A cewarsa:

“Mun yafe wa duk wadanda suka bar mu. Muna da yawa da suka dawo amma ina so ku je ku dawo da sauran.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An san jihar Bayelsa da siyasar jam’iyya ta cikin gida kuma duk mun san haka; wanda ke nufin da zarar ka daga tutar jam’iyya a kowane mataki, kawai kamar ka lashe babban zabe ne da kansa."

Har ila yau in jaridar Daily Report, yayin gabatar da rajistar membobin jihar, Diri ya ce:

"Wannan shine farkon nasarar PDP da nasarorin zabe a jihar da kuma Fadar Shugaban Kasa nan da 2023."

Bikin Sauya Sheka: Ministan Buhari Zai Koma Gida Jam'iyyar PDP

Shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Ribas, Desmond Akawor, ya nuna yakinin cewa ministan sufuri, Rotimi Amaechi, zai koma PDP, kamar yadda Punch ta ruwaito. A

Read also

Gwamnatin Kaduna Ta Bayyana Ranar Buɗe Makarantu, Ta Sanya Wa Ɗalibai Sabon Ƙa’ida

kawor ya faɗi hakane a wurin wani taro a ƙaramar hukumar Ikwerre yayin da yake karbar masu sauya sheka daga wasu jam'iyyun siyasa zuwa PDP.

Akawor yace:

"Yan uwanmu dake shigowa PDP, bara in faɗa muku wani abu, duk waɗannan shugabannin da kuke gani mambobin PDP ne, sun je can ne suga wainar da ake toyawa amma zasu dawo."

Kwarewa ya kamata a duba wajen tantance wanda zai gaji Buhari, in ji Yahaya Bello

A wani labarin, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce cancanta ya kamata ya zama babban abin da ‘yan Najeriya za su fi mayar da hankali a kai, yayin da suke zuwa rumfunan zabe don zaben wanda zai maye gurbin Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari, a 2023.

Ya fadi haka ne a jawabin da Shugaban Ma’aikatansa, Mohammed Abdulkareem ya yi a madadinsa a wani taron kwanaki biyu na jagorancin kasa kan zaman lafiya da tsaro da Majalisar Matasan Najeriya ta shirya.

Read also

Da dumi-dumi: Yan sanda sun ceto mutum 12 da aka sace a Zamfara

An gudanar da shirin ne a jihar Nasarawa, Lafia ranar Talata 17 ga watan Agusta, jaridar Punch ya ruwaito.

Source: Legit.ng News

Online view pixel