Gwamnatin Kaduna Ta Bayyana Ranar Buɗe Makarantu, Ta Sanya Wa Ɗalibai Sabon Ƙa’ida

Gwamnatin Kaduna Ta Bayyana Ranar Buɗe Makarantu, Ta Sanya Wa Ɗalibai Sabon Ƙa’ida

  • Gwamnatin Jihar Kaduna ta umurci makarantun sakandare su fara budewa daga ranar Laraba 18 ga watan Agusta
  • Hakan na zuwa ne bayan rufe makarantu a jihar sakamakon ayyukan da sojoji ke yi na yaki da yan bindiga da ke addabar mutane da sace dalibai
  • Amma wata sabuwar ka'ida shine gwamnatin ta umurci dalibai yan karamin aji 3 ne kawai za su koma makarantar kuma su rika zuwa da kayan gida

Kaduna, Jihar Kaduna - Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa za ta fara bude makarantu daga ranar Laraba, 18 ga watan Agustan shekarar 2021, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai, dai tace daliban da ke karamin aji na 3 wato JSS III ne kadai za su koma makarantun.

Gwamnatin Kaduna Ta Bayyana Ranar Bude Makarantu, Ta Sanya Wa Ɗalibai Sabon Ƙa’ida
Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A cewar rahoton da Daily Trust, Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Shehu Usman Muhammad ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Sabuwar ka'idar da aka saka wa daliban?

Ya kuma ce daliban da za su koma makarantun da kayan gida za su rika zuwa a maimakon unifom.

Gwamnatin jihar, a makon da ta gabata ta rufe makarantun ne sakamakon ayyukan da sojoji ke yi na yaki da yan bindiga a jihohin arewa maso yamma a kasar.

Muhammad ya ce:

"Gwamnati ta bada umurnin bude makarantu ga daliban JSS III, wadanda za su rubuta jarrabawar su ta NECO BECE da za fara a ranar 23 ga watan Agusta zuwa 6 ga watan Satumba.
"Don haka, ana umurtar bude makarantun sakandare domin daliban JSS III daga ranar 18 ga watan Agustan 2021 kuma su sanar da daliban su rika zuwa da kayansu na gida."

Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

A wani labarin daban, kun ji cewa Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma.

A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba kuma ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel