Da dumi-dumi: Yan sanda sun ceto mutum 12 da aka sace a Zamfara

Da dumi-dumi: Yan sanda sun ceto mutum 12 da aka sace a Zamfara

  • Yan sanda sun samu nasarar kwato mutum 12 hannun yan bindiga
  • Wannan ya biyo bayan bidiyon daliban da aka sace a kwalejin noma
  • Gwamnatin Zamfara ta lashi takobin ceto wadanda aka sace

Zamfara - Hukumar yan sandan jihar Zamfara ta samu nasarar ceto mutum 12 da yan bindiga suka sace a jihar Zamfara, kakakin hukumar Mohammed Shehu ya bayyana.

A jawabin da Shehu ya saki ranar Laraba, ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka ceto akwai shugaban masu gadin kwalejin ilmin kiwon lafiya dake Tsafe, jihar Zamfara.

Rahoto TheCable ya nuna cewa an yi awon gaba da shi ne da safiyar Laraba.

Shehu ya kara da cewa a harin ceto da suka kai, jami'an yan sanda sun samu nasarar ceto wasu mutum 11 da aka sace ranar 12 ga Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

Yace:

"Mun samu labarin cewa asu tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 11 a kauyen Yarkofoji, dake karamar hukumar Bakura ranar 12 ga Agusta, 2021."
"Bayan haka, hukumar ta samu nasarar ceto shugaban masu tsaron kwalejin fasahar kiwon lafiya dake Tsafe."

Kakakin yan sandan ya kara da cewa an garzaya da wadanda aka ceto asibiti domin duba lafiyarsu kafin mayar da su wajen iyalansu.

Da dumi-dumi: Yan sanda sun ceto mutum 12 da aka sace a Zamfara
Da dumi-dumi: Yan sanda sun ceto mutum 12 da aka sace a Zamfara
Asali: Original

Sun saki sabon bidiyon daliban da suka sace a kwalejin aikin noma dake Zamfara

A bangare guda, yan bindigan da suka yi awon gaba da dalibai da malamai a kwalejin aikin noma da kimiyar dabbobi, Bakura, sun saki bidiyon daliban dake hannunsu.

A cikin faifan bidiyon mai tsahon dakikai 30, daliban na kira ga gwamna Bello Matawalle ya taimaka ya biya kudin fansa, rahoton PremiumTimes.

Kara karanta wannan

A karshe ‘yan sanda sun cafke shahararrun masu garkuwa da mutane da ke addabar jihar Adamawa

A cikin bidiyon, an ga dalibai da ma'ikaata mata tsugunne a kasa idanuwansu a rufe kuma zagaye da yan bindigan masu rike da bindiga kirar AK47.

Sun Nemi a biyasu Miliyan N350m

Yan bindigan sun nemi a basu miliyan N350m kuɗin fansa kafin su sake daliban.

Da yake magana da Punch ta wayar salula, shugaban kwalejin, Alhaji Habibu Mainasara, yace barayin sun tuntuɓe shi ta wayar salula.

Yace yan bindiga sun nemi a ba su miliyan N350m kuɗin fansar mutum 20 dake hannun su a yanzun sannan su sako su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel