Kwarewa ya kamata a duba wajen tantance wanda zai gaji Buhari, in ji Yahaya Bello

Kwarewa ya kamata a duba wajen tantance wanda zai gaji Buhari, in ji Yahaya Bello

  • Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya shawarci 'yan Najeriya da su duba cancanta ba yanki ba wajen zaben shugaba
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wani taron da ya gudana jiya Talata a jihar Nasarawa, Lafiya
  • Gwamnan ya ce, ya kamata a ba matasa damar rike madafun iko a zaben shekarar 2023 mai zuwa

Nasarawa - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce cancanta ya kamata ya zama babban abin da ‘yan Najeriya za su fi mayar da hankali a kai, yayin da suke zuwa rumfunan zabe don zaben wanda zai maye gurbin Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a 2023.

Ya fadi haka ne a jawabin da Shugaban Ma’aikatansa, Mohammed Abdulkareem ya yi a madadinsa a wani taron kwanaki biyu na jagorancin kasa kan zaman lafiya da tsaro da Majalisar Matasan Najeriya ta shirya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

An gudanar da shirin ne a jihar Nasarawa, Lafia ranar Talata 17 ga watan Agusta, jaridar Punch ya ruwaito.

Kwarewa ya kamata a duba wajen tantance wanda zai gaji Buhari, in ji Yahaya Bello
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Yahaya ya bukaci shugabannin siyasa na kasar nan da su ba matasa dama don daukar matsayin shugabanci a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya ce:

"Zabin wanda zai zama Shugaban Najeriya na gaba a 2023 dole ne ya dogara da wanda ya dace ba wai yankin da ya fito ba."

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

Wani tsohon Ministan Ayyuka a Najeriya, Adeseye Ogunlewe, ya ce Kudu maso Gabas ba za su iya samar da shugaban kasar Najeriya na gaba ba saboda ba su da hadin kai.

Ya fadi hakan ne yayin wani shirin Arise TV mai suna 'The Morning Show' a ranar Laraba 11 ga watan Agusta, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu zai zama shugaban kasa nagari, in ji tsohon hadimin Jonathan, ya fadi dalili

A cewarsa, babu wani dan takarar da ya fi dacewa ya jagoranci kasar nan a 2023 fiye da tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu - wata sanarwa da Bode George, memba na kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, wanda shi ma ya kasance a cikin shirin.

Ya yi ikirarin cewa rashin iya jagoranci da rashin hadin kai zai yi tasiri kan duk wani dan takarar shugaban kasa na Kudu maso Gabas.

'Bani da burin zama shugaban kasa': Tsohon sarkin Kano Sanusi ya yi watsi da siyasa

A wani labarin, Tsohon Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Muhammmadu Sanusi II ya bayyana cewa baya son zama Shugaban kasa ko shiga harkar siyasa, The Nation ta ruwaito.

Don more lokacinsa, tsohon sarkin ya ce ya sami damar shiga Jami'ar London don karatu a shirin PhD a fannin Doka.

Zai yi rubutu kan "Kayyade dokokin iyali na Musulmi, kayan aikin gyara zamantakewa".

Kara karanta wannan

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

Da yake jawabi a wajen liyafar karrama shi don murnar cikarsa shekaru 60 a Abuja, Sanusi ii ya ce tsoro da kwadayi sune manyan abubuwa biyu da suka lalata Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.