Shugaba Buhari zai kai ziyarar ta'aziyya zuwa jihar Adamawa ranar Juma'a mai zuwa

Shugaba Buhari zai kai ziyarar ta'aziyya zuwa jihar Adamawa ranar Juma'a mai zuwa

  • A shirye-shiryen zuwan shugaba Buhari jihar Adamawa, rundunar 'yan sanda ta ce za ta tsaurara tsaro
  • Rundunar ta ce za ta tura jami'an ta da dama domin tabbatar da doka da oda a jihar gabanin ziyarar
  • Shugaba Buhari zai kai ziyarar ta'aziyya ne jihar Adamawa ga iyalai Ahmed Joda da ma 'yan jihar

Adamawa - Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta ce za ta tura dakarunta da yawa saboda ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa Yola a ranar Juma'a mai zuwa.

Kakakin rundunar, DSP Sulaiman Nguroje, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis 19 ga watan Agusta a Yola, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya shawarci jami’ai da su nuna matukar kwarewar aiki tare da yin aiki cikin yanayin doka yayin ziyarar.

Shugaba Buhari zai kai ziyarar ta'aziyya zuwa jihar Adamawa ranar Juma'a mai zuwa
Shugaba Buhari na shirin hawa jirgin sama | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Nguroje ya ce:

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Rundunar ta shirya tura dakarunta don sa ido da kuma kara karfin gwiwa don kiyaye zaman lafiyar jama’a.

Ya kuma bayyana cewa, rundunar 'yan sanda za ta tura jami'ai da kayan aiki daban-daban don tabbatar da tsaro a jihar.

Ya ce 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su yi aiki tare don tabbatar da doka da oda yayin ziyarar.

Mista Nguroje duk da haka ya yi kira ga jama'a da su hada kai da yin aiki tare da jami'an tsaro yayin gudanar da aikinsu na kiyaye doka da oda.

Shugaba Buhari zai yi ta'aziyya ga iyalai da jama'ar Adamawa kan rasuwar marigayi Ahmed Joda yayin ziyarar.

Ziyarar Shehu Dahiru Usman Bauchi zuwa fadar shugaba Buhari

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammdu Buhari (mai ritaya), ya karbi bakuncin jagoran darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Alhamis 19 ga watan Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya watsa hotunan ganawar tasu a kafar Facebook.

Ya rubuta cewa:

"Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shahararren Malamin Addinin Musulunci kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi a gidan gwamnati a ranar 19 ga Aug 2021."

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna juyayi ga iyalai da sauran wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su sakamakon ci gaba da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a makwannin da suka gabata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wannan lamarin da ya shafi dubban mutane a jahohi 32 na Najeriya, ya haifar da asarar gidaje, gonaki, rayuka da rushewar rayuwa ta yau da kullun.

Shugaban, wanda ya koma aiki a ranar Laraba bayan kebewa na kwanaki biyar bayan balaguro zuwa Landan, ya nuna damuwa kan halin da ake ciki, in ji News Diary.

Kara karanta wannan

Femi Adesina: Abin da ya sa aka ga Buhari ya je har gida ya ziyarci Tinubu kafin ya baro Ingila

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.