Tashin hankali a jihar Edo yayin da ake zargin kungiyar Arewa da yunkurin nada Sarki a masarautar Benin

Tashin hankali a jihar Edo yayin da ake zargin kungiyar Arewa da yunkurin nada Sarki a masarautar Benin

  • Zafafan kalamai sun biyo bayan shirin da wata kabila daga Borno ke yi na nada daya daga cikin membobinta a matsayin Sarkin Shuwa Arab
  • Wasu mazauna birnin Benin sun bayyana dalilin da ya sa ba za su bari a gudanar da bikin da aka shirya ba
  • Oba na Benin shi ne Sarki kuma mai kula da al'adun kuma shi aka sani a matsayin babban basarake a garin Benin

Birnin Benin, jihar Edo - Wasu kungiyoyi a jihar Edo sun yi watsi da shirin da wata kabila daga Borno na nada Idris Adanno a matsayin Sarkin Shuwa Arab na jihar Edo.

PM News ta ba da rahoton cewa labarin nadin sarautar da aka shirya yi a ranar Asabar, 21 ga watan Agusta, a wani yanki na birnin Benin, ya haifar da tashin hankali a jihar.

Tashin hankali a jihar Edo yayin da ake zargin kungiyar Arewa da yunkurin nada Sarki a masarautar Benin
Mazauna garin sun ce nadin sarautar wani yunkuri ne na haddasa fitina Hoto: Goliath Marcus Garvey, Alhji Umaru, Joshua David
Asali: Facebook

Mazauna birnin sun sha alwashin cewa ba za su bari a yi wannan nadin sarautar ba.

Katin gayyatar bikin nadin sarautar, wanda aka gani a Facebook, ya jawo fushi tsakanin matasa.

Shugaban kungiyar Benin Solidarity Movement (BSM), Elder Curtis Eghosa Ugbo, ya yi gargadin cewa 'yan asalin Benin za su yi duk abin da za su yi don hana nada wani sarki a cikin garin, jaridar The Punch ta ruwaito.

Ya ce:

"Wannan ba zai taba faruwa a masarautar Benin ba, mu Benin ne."

Wata kungiya, Great Benin Descendants (GBD), ta ce za ta toshe wurin da ake shirin nadin sarautar.

Babban jagoran kungiyar, Imasuen Izoduwa, ya bayyana taron a matsayin shirme. Ya ce garin Benin ba zai iya samun Oba da Sultan ba.

Wani shugaban matasa, Kwamared Amos Ehinomen Uagbor ya ce:

“Ana iya samun wannan a wani wuri? Shin ya kamata a yanzu mu samu OBA da Sultan a jihar Edo? A gaskiya, ya kamata a rufe wurin taron. ''

Batun ya kuma haifar da martani daga rukunin Facebook da aka sani da dandalin siyasar Edo.

Wani memba na ƙungiyar da ya wallafa kwafin gayyatar ya yi tambaya me zai sa Shuwa Arab su sami Sarki a masarautar Benin.

Ya ce:

"Akwai tambayoyi da yawa game da wannan: Me ke faruwa a nan?
"Me zai sa Shuwa Arab su sami Sarki a masarautar Benin? Me yasa Enogie na Eyaen zai ba da damar wannan taron a yankinsa da otal ɗinsa?
"Za mu iya gwada wannan a Arewa? ''

Wani mamba na kungiyar, Goliath Marcus Garvey, ya yi zargin cewa wani shiri ne na kwace masarautar Benin.

Ya ce:

'' Haka suka yi suka kama Illorin. Yanzu suna matsowa kusa.''

A wani labari na daban, mun ji cewa a yanzu haka, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin ganawa da manyan hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Har ila yau a wurin taron akwai Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, ya bayyana cewa a ganawar za a sanar da Shugaban kasar ci gaban da aka samu a yaki da ta'addanci a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel