Na shirya zuwa kurkuku da Jonathan ya tsige ni daga Gwamnan CBN inji Tsohon Sarki Sanusi

Na shirya zuwa kurkuku da Jonathan ya tsige ni daga Gwamnan CBN inji Tsohon Sarki Sanusi

Muhammadu Sanusi II yace ya yi tunanin za a jefa shi a gidan kurkuku a 2014

Tsohon Gwamnan na CBN ya samu matsala da Gwamnatin Goodluck Jonathan

Sanusi II ya taba shiga gidan yari, don haka ba ya tsoron a ce za a garkame shi

Abuja - The Sun ta ce tsohon gwamnan babban banki, Sanusi Lamido Sanusi wanda ake kira Muhammadu Sanusi II yanzu, ya tabo batun aikinsa a CBN.

Da yake jawabi a karshen makon da ya gabata, Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ya yi tunanin za a rufe shi a gidan kurkuku bayan barin CBN.

Tsohon Sarkin na Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi wannan bayani a wajen bikin da aka shirya a garin Abuja domin taya shi murnar cika shekara 60 a Duniya.

Kara karanta wannan

'Bani da burin zama shugaban kasa': Tsohon sarkin Kano Sanusi ya yi watsi da siyasa

Mai martaban yace ya fahimci akwai wadanda ba su jin dadi, idan ya yi magana, amma yace duk da haka ba zai fasa magana a kan rashin adalcin da ake yi ba.

Khalifan na Tijjaniya ya fada wa mutanen da suka halarci taron cewa ba ya tsoron barazana da gidan yari.

Tsohon Sarkin yake cewa tun da ya yi zaman gidan yari na sama da shekara daya a garin Sokoto a lokacin da yake cikin kuruciya, bai tsoron dauri a halin yanzu.

Tsohon Sarki Sanusi
Muhammadu Sanusi II da Goodluck Jonathan Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abin da Sanusi II ya fada a taro

“A lokacin da na samu matsala a babban bankin Najeriya, an fito ana ta surutu, na fada wa shugaban kasan cewa ba ya bukatar ya saurari surutan nan.”
“Kawai ya fada mani cewa zai jefa ni a gidan kurkuku na wasu shekaru. Zan mika kai na da kai na zuwa kurkukun, in zauna na shekarun da yake bukata.”

Kara karanta wannan

Sanusi II: Najeriya ba ta cimma komai ba cikin shekaru 40, dole na fadi gaskiya

“Bayan na fito daga gidan yari, zai cigaba da yin abin da na ke yi a yanzu.”
” Bayan mutuwa, babu azabtarwar da ta fi dauri muni. Idan ka ce za ka daure ni, an taba daure ni, iyakar ta kenan. Idan kace za ka kashe ni, kowa zai mutu.”

An rahoto Sanusi II yana cewa hadama da tsoro suna cikin abubuwan da suka hana tattalin arzikin Najeriya cigaba, yace sai an ci karfin hakan za ayi nasara.

Janar Babangida ya cika 80

A jiya shugaba Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Babangida murnar zagayowar ranar haihuwarsa, a wani jawabi da ya fitar a Abuja.

A jawabin Garba Shehu, Buhari ya yi wa Babangida addu’ar karin tsawon rai, yace shi da tsohon shugaban kasar sun zo daya a matsayinsu na tsofaffin sojojin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel