Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona

Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona

  • An birne tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ibrahim Mantu a garin Abuja a yau Talata
  • Mantu ya rasu ne bayan fama da yayi da gajeriyar rashin lafiya da aka gano cutar korona ce ta kama shi
  • Cike da kiyaye dokokin dakile korona, an ga jama'a sanye da takunkumin fuska kuma masu birneshi sanye da kayan kariya

FCT, Abuja - Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, an birne shi a Abuja bayan rasuwarsa a yau Talata da safe.

Kamar yadda thecable ta ruwaito, Mantu wanda ya rasu a sa'o'in farko na ranar Talata, an birne shi a makabartar Gudu kamar yadda dokokin kiyaye yaduwar korona suka tanadar.

Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona
Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona
Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da za ka sani game da rayuwar Marigayi Sanata Mantu da COVID-19 tayi ajalinsa

An gano cewa yayi kwanaki yana fama da rashin lafiya kuma ya rasu a wani asibitin kudi yayin da yake killace a Abuja, TheCable ta ruwaito.

Ga wasu daga cikin hotunan jana'izarsa da birne shi da aka yi inda aka ga masu makoki sanye da takunkumin fuska yayin da masu birne shi ke sanye da kayan kariya.

Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona
Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona
Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An bada sanarwar za a yi wa Sanata Ibrahim Mantu sallah a gidansa da ke Apo, birnin Abuja.

Legit.ng Hausa ta tsakuro kadan daga cikin wannan dattijo, fitaccen ‘dan siyasa, kuma daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya.

Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona
Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An haifi Ibrahim Mantu a ranar 16 ga watan Fubrairu, 1947, a kauyen Chanso, a yankin Gindiri, karamar hukumar Mangu, jihar Filato.

Rahotanni sun ce Sanata Mantu ya rasu ya na da shekara 74 bayan ya yi jinyar COVID-19.

'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi awon gaba da kayan abinci a Abuja

Kara karanta wannan

'Bani da burin zama shugaban kasa': Tsohon sarkin Kano Sanusi ya yi watsi da siyasa

Masu garkuwa da mutane sun harbe wani matashi, Haruna Dako, sannan sun sace kayan abinci iri-iri a Kambu dake wuraren Abaji a birnin tarayya, Abuja.

Daily Trust ta ruwaito yadda kauyen Kambu, wanda yake karkashin Chakumi yakeda iyaka da Gwagwalada, inda Rafin Gurara yake gudana tsakanin garuruwan.

Mazaunin garin mai suna Yahaya ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 10:27 na dare lokacin da masu garkuwa da mutane suka shigo garin da yawansu.

Marigayin ya fito daga gidansa ne ya kai cajin wayarsa wani shago, kwatsam masu garkuwa da mutanen suka tsare shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel