Da duminsa: Hotuna sun billo yayin da gadar Mokwa/Jebba ta rushe, masu amfani da titin sun tarwatse don tsira

Da duminsa: Hotuna sun billo yayin da gadar Mokwa/Jebba ta rushe, masu amfani da titin sun tarwatse don tsira

  • Motoci sun makale yayin da wata gada ta balle a kauyen Tatabu da kauyen Gida Moin da ke kan hanyar Jebba/Mokwa/Kotangora a jihar Neja
  • An tattaro cewa hukumar bayar da agaji na nan suna kokari don tabbatar da ganin cewar ba a rasa rai ba
  • An bukaci masu bin hanyar da su karkata zuwa wata hanya ta daban don isa wuraren da suke son zuwa

Rahoton da ke isowa Legit.ng na nuni da cewa wasu motoci sun makale bayan rushewar wata gada a kauyen Tatabu da kauyen Gida Moin da ke kan hanyar Jebba/Mokwa/Kotangora a jihar Neja.

Har yanzu ba a san musabbabin faduwar gadarba ba a lokacin kawo rahoton, amma an shawarci masu amfani da hanyar da su nemi wata hanya ta daban don isa wuraren da suke son zuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayin da ‘yan bindiga suka bude wuta kan matafiya a Jos

Da duminsa: Hotuna sun billo yayin da gadar Mokwa/Jebba ta rushe, masu amfani da titin sun tarwatse don tsira
Gadar hanyar Mokwa/Jebba ta rushe
Asali: Original

Wani sako da aka aika wa Legit.ng daga wani mazaunin Abuja, ya bayyana cewa masu ababen hawa da ke zuwa jihar Neja da kewayenta na iya ɗaukar hanyar Abuja/Lokoja don gujewa fadawa tarko yayin da jami'an hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA) ke kokarin hana asarar rayuka.

Sakon ya ce:

"Wannan don sanar da jama'a ne game da halin da hanyar Jebba/Mokwa/Kotangora a jihar Neja ke ciki. A halin yanzu gadar dake Tatabu da kauyen Gida Moin ta rushe, hanya daya tilo da ta ke mafiya a yanzu ita ce hanyar Abuja/Lokoja. Da fatan za a aika da wannan sako ga wasu."

Jihohi bakwai da suka yi kaurin suna wajen lalacewar hanyoyi a Najeriya

Rashin kyawun hanyoyi ba sabon labari ba ne game da kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai a jihar Katsina

Tsawon shekaru, ’yan Najeriya sun samu kansu cikin mawuyacin yanayi wanda ke tattare da bin kan wadannan hanyoyi: da dama sun rasa ’yan uwansu na kusa da muhimman abubuwa masu alfanu a garesu da ma wasu ababuwan sakamakon hadurran da ke faruwa a kai a kai saboda lalacewar hanyoyin.

Koda yake, yanzu ya zamewa direbobin Najeriya jiki su koyi yadda za su sarrafa motocinsu lokacin da suke tuki a kan wadannan matattun hanyoyin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng