Jihohi bakwai da suka yi kaurin suna wajen lalacewar hanyoyi a Najeriya — Rahoto
- A wasu jihohin lalacewar hanyoyin ya zama tamkar ba a ma taba yin su ba a wajen
- Jihar Legas kusan ita ce kan gaba a lalacewar hanyoyin mota
- A wasu jihohin kuma al’ummin jihohin sun ma saba da yanayin lalacewar titunan ta yadda abin ya zama musu jiki
Rashin kyawun hanyoyi ba sabon labara ba ne game da kasar Najeriya.
Tsawon shekaru, ’yan Najeriya sun samu kansu cikin mawuyacin yanayi wanda ke tattare da bin kan wadannan hanyoyi: da dama sun rasa ’yan uwansu na kusa da muhimman abubuwa masu alfanu a garesu da ma wasu ababuwan sakamakon hadurran da ke faruwa a kai a kai saboda lalacewar hanyoyin.
Koda yake, yanzu ya zamewa direbobin Najeriya jiki su koyi yadda za su sarrafa motocinsu lokacin da suke tuki a kan wadannan matattun hanyoyin.
A wani rahoto da wata kungiya mai suna Nigeria Abroad ta fitar ta bayyana hanyoyin da suka hanyoyi mafi muni a jihohi bakwai a fadin kasar. Hanyoyin sun nuna sanannun kuma munanan ramuka da ramuka masu cin mota da kuma ramuka masu kisa.
Ga jerin jihohin da suka yi kaurin suna ta fuskar munin hanyoyin mota a Najeriya:
1. Jihar Abia
Duk da taken da ake mata na: 'Jihar Allah', hanyoyin mota a jihar sun fuskanci rashin kula daga gwamnatocin jihar da suka gabata, wadanda suka ki yin 'aikin Allah' a jihar.
Hanyoyin Jihar Abia sun lalace sosai ta yadda idan ana ruwan sama, kusan da wuya a iya tuka mota. Ambaliyar ruwa ta zama ruwan dare, wasu lokatun kuma sharar kan tituna kan kara tabarbarewar yanayin. 'Yan jihar sun yanke kauna da mahunkuntan jihar ta yadda da yawa ba sa yin kuka game da rashin kyakkyawan shugabanci.
2. Jihar Edo
Hanyoyin mota a jihar marasa inganci ne sai dai sun zama jiki a rayuwar al’ummar jihar. Ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni sun mayar da sanya silifas din roba wani bangare na kayan zuwa ofisoshinsu saboda wannan yana sa saukake musu shiga cikin kududdufin kan tituna da ruwan sama ya haifar.
Birnin Benin yana da mafi munin lamarin, ta yadda da wuya a ka ce idan ba haka birnin yake a koda yaushe ba.
3. Jihar Imo
Yanayin tituna a Owerri, babban birnin Jihar Imo sun yi lalacewar da har ta kai ga mazauna jihar ke bullo da wasu kananan hanyoyi na a wuraren da lalacewar ya yi munin gaske.
DUBA NAN: Najeriya ce kan gaba a yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara - Ministan Ilimi
DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara
4. Jihar Anambra
Hanyoyin Ekwulobia da Oko da Isuofia da kuma Igboukwu a Jihar Anambra zaizayar kasa ya cinye su inda mutum zai ga alamu tamkar girgizar kasa ce ta faru a wajen. Hakan na faruwa ne duk da cewa jihar na amfana da Kudin Asusun Kula da Iftila’i na Najeriya.
Jihar ta kasance guda cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a Najeriya. Tana da babbar kasuwa a Yammacin Afirka wato Babbar Kasuwar Onitsha.
5. Jihar Legas
Jihar Legas ana mata lakabi da sunan Babbar Cibiyar Kasuwanci da take da yawan al’ummar da aka kiyasta yawanta ya kai mutum miliyan 20. Sai dai duk da hakan, Jihar Legas watakila ma a iya cewa ita ce kan gaba a lalacewar hanyoyi a jihohin Najeriya. Watakila hakan bai rasa nasaba da yawan cunkoson ababen hawa a koda yaushe da ke zuwa tashoshin ruwan Apapa.
6. Jihar Ribas
A babban birnin jihar Fatakwal, mazauna birnin sun saba da dabarun kauce wa hawa kan tituna yayin da suke tuka manyan motoci da jifa-jifai da kananan motocin hawa.
Galibin masu amfani da kananan motoci ’yan tasi ne wadanda sun san yadda za su kula da motocin nasu.
Ramukan titunan birnin sun yi munin da kai ka ce an haka su ne yayin da al’ummar jihar suke sharar bacci, idan kuwa ka shiga kananan garuruwan abin ya fi haka muni.
7. Jihar Benuwai
Galibin hanyoyin gwamnatin tarayya a Jihar Benuwai sun yi lalacewar da mutane ba za su ko iya maleji da su ba sakamakon daukar shekaru ba tare da ana kulawa da su ba.
Hanyoyin sun zama cikin halin takaici na tsawon lokaci. Hanyoyin zuwa babban birnin jihar Makurdi da Otukpo da sauransu sun yi lalacewar da ta wuce a ce sun baci inda suka zama a wanke ta yadda kai ka anya an taba samun titi a wajen kuwa.
Asali: Legit.ng