Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayin da ‘yan bindiga suka bude wuta kan matafiya a Jos

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayin da ‘yan bindiga suka bude wuta kan matafiya a Jos

  • 'Yan bindiga sun bude wuta a kan wasu matafiya a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato
  • Matafiyan na a hanyarsu ta dawowa daga wani taro na sabuwar shekarar Musulunci a Bauchi
  • An tattaro cewa ba a ga wasu da dama ba daga cikin mutanen da harin ya rutsa da su

Akalla matafiya 15 ne aka kashe yayin da ba a ga wasu da dama ba a yankin Gada-biyu na Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Jihar Filato.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wadanda abin ya rutsa da su suna hanyarsu ta Jos lokacin da suka hadu da ‘yan bindigar da suka budewa motocinsu wuta.

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayin da ‘yan bindiga suka bude wuta kan matafiya a Jos
An harbe wasu matafiya a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ba a san inda wasu daga cikin wadanda abin ya rutsa da su suke ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

Majiyoyin tsaro sun shaida wa jaridar cewa an ajiye gawarwaki akalla 15 a dakin ajiye gawa na asibitin kwararru na Filato.

Muhammad Ibrahim, daya daga cikin fasinjojin, wanda ya tsere daga harin, ya ce suna cikin ayarin motocin bas guda biyar mai cin mutane 18 lokacin da maharan suka kai hari.

Yace suna dawowa daga jihar Bauchi inda suka halarci wani taron tunawa da sabuwar shekarar musulunci.

Ibrahim ya ce taron ya gudana ne a masallacin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a jihar Bauchi.

Ya ce:

"Mun ci karo da gungun 'yan bindigar ne a yankin Gada-Biyu na karamar hukumar Jos ta Arewa.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, ya shaida wa Daily Trust cewa an tura jami’an tsaro yankin.

Amma, ya ce ba shi da cikakken bayani game da lamarin kuma ya yi alkawarin cewa zai waiwayo da zaran an samu bayanai.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

An kuma tattaro cewa tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ta Filato da wasu manyan jami’an tsaro a jihar suka ziyarci asibitin don gane wa idonsu yadda lamarin ya faru.

Kashe-kashen dake faruwa a Plateau ya saba dokokin Allah, Malaman addinai sun yi tsokaci

A wani labarin, majalisar Malaman addinai a jihar Plateau ta yi Alla-wadai da kashe-kashe da asarar gonaki, gidaje da sauran dukiyoyi dake faruwa a wasu sassan jihar kwanakin nan.

Majalisar a jawabin da ta saki ranar Juma'a a Jos kuma shugabanninta Pandang Yamsat da Muhammadu Haruna, suka rattafa hannu, sunce wannan kashe-kashe ya saba dokokin Allah, rahoton DN.

Yamset Pandang shine tsohon shugaban cocin COCIN, yayinda Mohammadu Haruna shine Sarkin Wase kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam, JNI, a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel