Ambaliya: Ruwan sama yayi awon gaba da sansanin 'yan gudun hijira a Borno
- Rahotanni sun tabbatar da yadda ruwan saman da aka yi ranar Talata da yamma yayi sanadiyyar rasa matsugunnin ‘yan gudun hijira
- Ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya ya rutsa da kimanin ‘yan gudun hijira 6,830 dake zaune a sansaninsu na Bakassi
- Sun shiga tsaka mai wuya sakamakon rashin makwanci da kuma fargabar barkewar annobar cutar kwalara da ta yawaita a garuruwa
Bakassi, Borno - Dubban ‘yan gudun hijira dake jihar Borno sun shiga tsaka mai wuya sakamakon mamakon ruwan sama da ya barke a ranar Talata da yamma.
Rahotanni sun tabbatar da yadda aka tafka ruwa kamar da bakin kwarya wanda yayi ta ambaliya a yankin, Daily Trust Aminiya ta ruwaito.

Asali: UGC
‘Yan gudun hijirar sun shiga mummunan yanayi akan rashin wurin kwana da fargabar barkewar annobar kwalara, Daily Trust Aminiya ta ruwaito.
An samu tattaunawa da wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar inda aka gano cewa ruwa ya mamaye ofisoshi da duk wasu matsugunai da kungiyoyi suka agaza suka gina musu.
Dalla-dalla yadda lamarin ya auku
Daya daga cikin ‘yan gudun hijirar, Bura Kaka ya yi kira ga gwamnati da sauran kungiyoyi da su taimaka su gina musu matsugunnin da zasu raba a Bakassi.
Tun karfe 4:50 na yamman ranar Talata ruwa ya barke mai yawa kamar da bakin kwarya. Hakan ya janyo ambaliya musamman ga masu kwana a tantina.
Gaba daya sansanin ya cika makil da ruwa. Muna bukatar taimako na gaggawa daga gwamnati da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka mana don har yanzu ba a gama ruwan ba.
Muna rokon masu hannu da shuni da gwamnati ta kalli mummunan yanayin da muke ciki da kuma barkewar cutar kwalara da zazzabun cizon sauro da yake ta bulla wuri-wuri ta agajemu,” a cewar Kaka.
Bayan aukuwar lamarin, wani jami’in hukumar bada agaji cikin gaggawa ta kasa (NEMA), ya tabbatar da cewa hukumarsu tare da hadin kan SEMA ta jihar sun hada karfi da karfe wurin kai dauki ga ‘yan gudun hijirar dake Bakassi.
Sojoji sun cafke mutum 8 da ake zargi da hannu a bindige mata 3 a Bassa, Filato
Rundunar Operation Safe Heaven a ranar Talata, 10 ga watan Augustan 2021 ta kama mutane 8 da ake zargin suna da hannu a harbin wasu mata 3 a wata gona dake kusa da Rafin Bauna dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato.
Rundunar ta amsa kiran gaggawar da aka yi mata akan kisan mata 3 da suke kusa da Rafin Bauna wadanda wasu ‘yan bindiga suka harbe, PR Nigeria ta ruwaito.
Take anan rundunar tayi gaggawar isa wurin inda ta riski mata 3 cikinsu har 2 sun mutu daya kuma rai a hannun Allah.
Asali: Legit.ng