Sojoji sun cafke mutum 8 da ake zargi da hannu a bindige mata 3 a Bassa, Filato

Sojoji sun cafke mutum 8 da ake zargi da hannu a bindige mata 3 a Bassa, Filato

  • Rundunar Operation Safe Heaven ta kama mutane 8 da ake zargin sun harbe wasu mata 3 a wata gona dake kusa da Rafin Bauna a karamar hukumar Bassa dake jihar Filato
  • Rundunar ta amsa kira bayan an tabbatar mata da kisan matan 3 a ranar Talata wadanda suka mutu take yanke bayan sun sha harbi a wurin ‘yan ta’addan
  • Yanzu haka mutane 8 din da ake zarginsu da harbin matan suna hannun jami’an OPSH suna cigaba da fuskantar tambayoyi da bincike mai tsanani

Bassa, Filato - Rundunar Operation Safe Heaven a ranar Talata, 10 ga watan Augustan 2021 ta kama mutane 8 da ake zargin suna da hannu a harbin wasu mata 3 a wata gona dake kusa da Rafin Bauna dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

Rundunar ta amsa kiran gaggawar da aka yi mata akan kisan mata 3 da suke kusa da Rafin Bauna wadanda wasu ‘yan bindiga suka harbe, PR Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun damke babban limamin IPOB da layu tare da harsasai

Sojoji sun cafke mutum 8 da ake zargin da bindige wata mata a Bassa, Filato
Sojoji sun cafke mutum 8 da ake zargin da bindige wata mata a Bassa, Filato. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sojoji sun gaggauta kai dauki bayan an kira su

Take anan rundunar tayi gaggawar isa wurin inda ta riski mata 3 cikinsu har 2 sun mutu daya kuma rai a hannun Allah.

Take anan aka dauketa aka kaita asibiti amma ana cikin magani ta rasu. Sun bincike gaba daya wurin inda suka kama mutane 8 da suke zargin suna da masaniya akan harbin. Yanzu haka suna hannun OPSH kuma suna shan tambayoyi.

OPSH ta magantu

Kwamandan OPSH, Manjo janar Ibrahim Ali ya ce zasu cigaba da sanya ido don ganin sun kawo karshen ta’addanci a unguwanni.

Kwamandan ya shawarci mutane da su yi amfani da layukan da aka raba musu don su sanar da hukuma idan sun ga wani abin zargi kusa dasu.

Kamar yadda PR Nigeria ta ruwaito, ya tabbatarwa da al’umma cewa zai yi iyakar kokarinsa wurin kawo kwanciyar hankali a jihar Filato da kewaye.

Jirgin NAF yayi luguden wuta a dazukan Niger, 'yan bindiga 70 sun sheka lahira

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Wani ya yi wuf da jarumar fina-finan Hausa, Diamond Zahra

Ayyukan hadakar sojojin sama dana kasa na Operation Gama Aiki (OPGA) suna kara samar da nasarori na ban mamaki.

PR Nigeria suna cigaba da tattaro bayanai akan yadda ‘yan bindigan dake da sansani a yankin Jasuwan Garba-Urege a jihar Neja sun sha ragargaza a wurin sojojin sama na OPGA da suka yi amfani da Agusta 109 da EC 135 jiragen yaki.

Wani babban jami’in tsaro wanda har da shi aka yi ragargazar ya ce sai da jirgin saman ya bi a sannu wurin gano asalin wuraren da miyagun mutanen suka yi dandazo sannan ya harba abubuwa masu fashewa a wuraren.

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel