'Yan Boko Haram 605 sun mika wuya ga sojoji, yunwa da annoba sun dira sansaninsu

'Yan Boko Haram 605 sun mika wuya ga sojoji, yunwa da annoba sun dira sansaninsu

  • Miyagun 'yan Boko Haram 605 sun mika makamansu tare da kansu ga dakarun sojin Najeriya a Borno
  • Kamar yadda aka gano, tsabar yunwa tare da miyagun cutukan da suka sauka a sansanoninsu shine babban dalilin tubansu
  • Wani jami'in sirri ya tabbatar da cewa ayyukan soji na sirri ne ke aiki duk da cike da salo da kwarewa suka yi, ga sakamako ana gani

Maiduguri, Borno - A cikin nasarorin da rundunar sojin Najeriya ke samu na kwanakin nan, a halin yanzu sun karba tubabbaun 'yan ta'addan Boko Haram 605 wadanda suka mika makamansu tare da mika wuya ga rundunar, PRNigeria ta tabbatar da hakan.

Ta kara da tattaro cewa an mika tubabbun 229 da suka hada da mata da kananan yara hannun gwamnatin jihar Borno.

A cikin makonnin nan, da yawan mayakan ta'addanci na Boko Haram da iyalansu sun sanar da tubansu kuma sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban mai hada bama-bamai na Boko Haram ya tuba tare da yaransa, ya mika wuya ga sojoji

'Yan Boko Haram 605 sun mika wuya ga sojoji, yunwa da annoba sun dira sansaninsu
'Yan Boko Haram 605 sun mika wuya ga sojoji, yunwa da annoba sun dira sansaninsu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Babban jami'in sirri yayi bayani dalla-dalla

Wani babban jami'i da ke da hannu cikin karbar tubabbun, ya sanar da PRNigeria cewa wannan karban tubabbun da iyalansu da ake yi, ya yi daidai da dokokin duniya kuma hakan ne ya dace a yi wa duk makiyin da ya tuba.

Kamar yadda babban jami'in yace, wasu daga cikin 'yan ta'addan suna tsoron za a kashesu amma kwarin guiwan matansu da iyayensu yasa suka tuba.

Su waye suka baiwa 'yan ta'addan kwarin guiwa?

Jami'in ya ce:

Abun mamaki, iyayensu da matansu ne suka basu kwarin guiwa cewa zasu tsaya tare dasu idan suka mika wuya.
Ba dole a ido a ga ayyukan sirrin da muka yi ba, amma ga sakamakonsu nan muna gani. Shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya ya bamu dabaru wadanda muka aikata kuma yace mu karba duk wanda ya tuba amma kada mu sassautawa wadanda suka yi taurin kai.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yiwa Boko Haram lugude, sun samo makamai, maganin karfin maza da littafin hada bam

Kokarin dakarun sojin ya hana 'yan ta'addan sakat kuma tuni suka fito daga maboyarsu suke mika makamansu.
A lokacin da suka iso, mun samu wasu kwamandoji da yunwa, ciwo da tsabar tsoro yasa suka tuba. Kafafen yada labarai na mana kokari yayin da 'yan kasa suka matukar yadda da ayyukanmu," yace.

Obasanjo ya lallaba Kwatano domin nemawa Igboho mafaka da afuwa

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasabjo ya kai ziyara jamhuriyar Benin a makon farko na Augustan 2021 kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Manyan majiyoyi sun sanar da theCable cewa sai da tsohon shugaban kasar ya biya ta tsibirin Zanzibar dake Tanzania a ranar 1 ga watan Augusta kafin ya wuce Benin din.

Ya kai ziyarar ne don yin ta'aziyya ga Nicephore Soglo wanda bai dade da rasa matarsa Roseline Soglo ba. Roseline ta rasu ne a ranar 25 ga watan Yuli tana da shekaru 87 a Cotonou.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel