SWC ta dakatar da Shugaban APC mai yi wa Buhari fatan ya mutu, Osinbajo ya hau mulki
- Wani faifai da ke yawo ya fallasa shugaban APC ya na wasu munanan kalamai
- Ana zargin shugaban jam’iyyar APC a Yola ya na fatan shugaban kasa ya mutu
- Jam’iyyar APC ta nada kwamiti na musamman da zai binciki Sulaiman Adamu
Adamawa – A jiya ne jam’iyyar APC ta dakatar da shugabanta na rikon kwarya na karamar hukumar Yola ta kudu, jihar Adamawa, Alhaji Sulaiman Adamu.
Gidan talabijin na TVC ya kawo rahoto a ranar Talata, 10 ga watan Agusta, 2021, cewa an dauki matakin nan ne saboda zargin Sulaiman Adamu da ake yi da laifi.
SWC ta sa kwamiti da zai yi bincike
Ana tuhumar shugaban jam’iyyar da laifin zagin Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari, don haka majalisar gudanar wa a jiha ta kafa kwamitin ladabtar wa.
TVC ta ce a wajen taron SWC na jihar Adamawa, an nada kwamitin mutum bakwai a karkashin jagorancin Sa’idu Naira da zai binciki zargin da ke wuyan Adamu.
Kwamitin Sa’idu Naira zai binciki Sulaiman Adamu da sauran abokan tafiyarsa kan zargin rashin da’a.
Jam’iyyar APC ta jihar Adamawa ta kafa wannan kwamiti ne bayan wani faifai da aka samu wanda aka ji wani ya na cewa ina ma Muhammadu Buhari ya mutu.
Abin da APC ta fada bayan taron gaggawa?
APC ta reshen jihar ta fitar da jawabi ta hannun sakataren yada labarai na riko, Mohammed Abdullahi.
“A matsayinmu na jam’iyya, mun samu wani faifai da ke yawo a kafen sadarwan zamani da aka ce ya fito ne daga wajen taron ‘ya ‘yanmu a Yola.”
“A dalilin wannan, mu ka yi taron SWC na gaggawa a yau (10/8/2021), inda aka saurari faifan sautin da kyau, aka maimaita, aka dauki mataki.”
“A karshe mun lura kalaman da aka yi amfani da su, suna da takaici, don haka mun bukaci ayi bincike.”
Bayan dakatar da Adamu da aka yi, domin ayi bincike da kyau, an ce mataimakinsa, Adamu Majekano ya dare kujerarsa a matsayin mukaddashin shugaban riko.
Me aka ji jigon na APC ya na fada?
A faifan an ji Adamu yana cewa da so samu ne, Coronavirus ta kashe shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, sai mataimakinsa Yemi Osinbajo ya hau mulki.
Jigon na APC ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na manyan masu ruwa da tsaki na APC, har da tsohon gwamnan Adamawa, Sanata Muhammadu J. Bindow.
Asali: Legit.ng