Dubbannin Mambobin Jam'iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar Hamayya YPP
- Daruruwan mambobin jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kwara sun fice daga cikinta zuwa YPP
- Kungiyar KSTF ta bayyana cewa sun yanke wannan hukuncin ne bisa yanayin yadda suka ga ana ware su a APC
- Shugaban KSTF, Abdulfatah AbdulRahman, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Ilorin
Kwara - Dubbannin mambobin jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta YPP a jihar Kwara, kamar yadda the nation ta ruwaito.
This day ta rahoto cewa, kungiyar waɗanda suka sauya shekar da ake kira 'Third Force' (KSTF) sun bayyana cewa dalilin rikicin APC yasa suka fice daga cikinta.
Hakanan sabbin mambobin YPP ɗin sun sha alwashin kwace mulki daga hannun APC a jihar a babban zaɓen 2023 dake tafe saboda kusoshin tafiyar O to Ge sun koma YPP.
Tafiyar O to Ge (Mun gaji hakanan) wani sabon salon yakin neman zaɓe ne da APC ta yi amfani da shi lokacin yakin neman zaɓe 2019 wanda ya taimaka sosai wajen samun nasarar APC a kowane mataki a Kwara.
Wane dalilai suka sa Mambobin suka sauya sheka?
Shugaban ƙungiyar, Abdulfatah AbdulRahman, wanda ya zanta da manema labarai a Ilorin, yace:
"Gazawar jam'iyyyar APC wajen adalci, da kuma kin nuna banbanci tsakanin mambobinta ne manyan dalilan ficewarsu zuwa YPP."
"APC ta ware mafi yawan mambobin ta daga bada gudummuwarsu wajen rijistar zama ɗan jam'iyya. Saboda haka muna ganin gwamnatin yanzun a jihar Kwara bata shirya sauke nauyin dake kanta ba a zaɓe mai zuwa."
Gwamnatin APC ba zata iya cika muradan al'umma ba
AbdulRahman, wanda ya tsaya takarar sanatan Kwara ta tsakiya a zaɓen 2019 ya bayyana cewa muradin mutanen Kwara na samun kyakkyawan shugabanci ba zai samu ba karkashin gwamnatin APC.
Yace:
"Sabida waɗanda dalilin ne yasa muka duba wace jam'iyya ce take wa mambobinta adalci, kuma muka duba kowace jam'iyya mai rijista a Najeriya."
"Daga karshe muka zakulo jam'iyyar da ta tabbatar mana zata baiwa kowane mamba hakkinsa tun daga maza, mata, matasa, tsofaffi, masu kuɗi da talakawa."
A wani labarin kuma Rikicin Siyasa ya barke a Enugu inda Mambobin Kwamitin Zartarwa Sun Tsige Shugaban Jam'iyyar APC
Yan kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC a jihar Enugu sun kaɗa kuri'ar tsige shugaban APC na jihar.
Kwamitin ya zargi tsohon shugaban da nuna rashin ɗa'a da kuma fatali da dokokin APC wajen gudanar da gangami.
Asali: Legit.ng