Da so samu ne, da Korona ta kashe Buhari mun huta: Shugaban APC a Yola

Da so samu ne, da Korona ta kashe Buhari mun huta: Shugaban APC a Yola

  • Jigogin APC sun bayyana rashin jin dadinsu ga shugaba Buhari
  • Wannan ba shi ne karo na farko da wasu jigogin APC za suyi kalamai irin wannan ba
  • A kwanakin baya, dan majalisar wakilai na Katsina yayi magana makamancin haka

Shugaban rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a karamar hukumar Yola ta kudu, Sulaiman Adamu, ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari, DailyNigerian ta ruwaito.

Adamu yace da so samu ne, da cutar Korona ta hallaka Buhari mataimakinsa Yemi Osinbajo ya hau kujerarsa.

A cewar majiyoyi, Jigon APCn ya bayyana hakan ne a ganawar wasu manyan masu ruwa da tsaki a jihar, ciki har da tsohon gwamnan Adamawa, Muhammadu Bindow da tsohon Kakakin majalisar jihar Adamawa, Kabiru Mijinyawa.

Sauran jigogin APC dake zaman sun hada da Yusha'u Adamu da Abubakar Sirimbai.

Majiyoyi da suka shaida wannan lamari sun ce an yi zaman ne ranar Lahadi, 8 ga Agusta, a gidan tsohon kwamishanan kananan hukumomin jihar Adamawa, Mustapha Barkindo-Mustapha da yamma.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Attajirin Dan Kasuwa, Okunbo, Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Shugaba Buhari Ya Yi Jimami

A faifan bidiyo da DailyNigerian tace ta samu, jigogin APCn sun caccaki shugaba Muhammadu Buhari.

A yaren Fulfulde, an yi Sulaiman Adamu na cewa:

"Ban san abinda ya sa Korona bata kashe Buhari ba. Da za'a ajiye Buhari da Osinbajo, zan zabi Osinbajo in bar Buhari."

Da so samu ne, da Korona ta kashe Buhari mun huta: Shugaban APC a Yola
Da so samu ne, da Korona ta kashe Buhari mun huta: Shugaban APC a Yola Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Babu abinda Buhari ya tsinanawa Adamawa, Sirimbai

Abubakar Sirimbai kuma yace gwanda "tsinannen shugaban kasan" ya mutu saboda Osinbajo ya hau mulki.

Yace:

"Gwanda tsinannen shugaban kasan ya mutu saboda mataimakinsa ya hau. Mun sayar da dukiyoyinmu domin taimakawa shugaban kasa yaci zabe."
"Babu abinda Buhari ya amfanawa Adamawa a shekaru shida da suka wuce. APC a Adamawa na rayuwa ne kawai don kokarin Bindow. Mun ji cewa Buhari na jin dadi idan yaji mutum ya talauce. Ba zamu rika bauta mai kamar yadda wasu ke yi ba."

Tsohon Kaakin majalisar dokokin jihar, Mijinyawa, a jaddada abubuwan da suka fada yace "Osinbajo ne namu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel