Shugaban Jam'iyyar APC, mambobin majalisar zartarwa duk sun yi murabus, sun koma PDP a Benue

Shugaban Jam'iyyar APC, mambobin majalisar zartarwa duk sun yi murabus, sun koma PDP a Benue

  • Jam'iyyar APC ta yi babban rashi a jihar Benue
  • Wannan ya biyo bayan rikicin dake gudana a uwar jam'iyyar APC
  • Daga cikin masu murabus akwai tsohuwar Sanata data wakilci Arewa maso gabashin jihar

Benue - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na karamar hukumar Kwande, a jihar Benue, Mr. Iorfa Dzoho, mambobin kwamitinsa, da wasu mambobin majalisar zartarwa sun yi murabus daga kujerunsu.

Dukkansu sun yi alkawarin cewa zasu koma jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ranar Asabar.

Sun yi wannan alkawari ne ranar Laraba a farfajiyar Kumakwagh dake Azaibo inda suka mika takardun murabus dinsu.

Mrs. Adzape-Orubibi, wacce itace tsohuwar Sanatan mai wakiltar Arewa maso gabashin Benue ce ta shirya taron domin sanar da al'ummarta cewa ta fita daga APC.

Shugaban Jam'iyyar APC, mambobin majalisar zartarwa
Shugaban Jam'iyyar APC, mambobin majalisar zartarwa duk sun yi murabus, sun koma PDP Hoto APC Benue
Asali: Facebook

Shugaban APC na Kwande, Dzhoho, ya ce shi da mambobin kwamitinsa sun yanke shawarar fita daga jam'iyyar APC ne saboda an mayar da su saniyar ware a zabukan sabbin shugabanni da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Wata babbar jigon PDP ta sauya sheka zuwa APC, ta bayyana dalilanta

Ya ce gwamnan jihar, Samuel Ortom, ya basu tabbacin cewa zai yi maraba da su idan suka shiga PDP kuma sun yi imani da shi saboda mai cika alkawura ne.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Wase Orbunde, Imo Doodi, Alago Azege, Bem Asule, Agbidye Waya da Mrs. Dion Imbor.

Rikici ya barke cikin uwar jam'iyyar PDP

A bangare guda, rikici ya barke a cikin gidan uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP.

Silar rigimar da ake yi a jam’iyyar hamayyar ita ce wasu gungu ba su tare da Prince Uche Secondus, wanda ke neman ya zarce a kujerarsa a zaben Disamba.

Daga cikin manyan zargin da ake yi wa shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus, akwai rashin gaskiya da rike amana wajen kula da baitul malin jam’iyya.

Shugabannin PDP da suka yi murabus a cikin makon nan sun karfafa wannan zargi, bayan cewa ba a tafiya da su, suna zargin Uche Secondus da cin kudin jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel