Dakarun Sojoji Sun Kutsa Daji Ta Sama da kasa, Sun Ragargaji Yan Bindiga Fiye da 45 a Zamfara

Dakarun Sojoji Sun Kutsa Daji Ta Sama da kasa, Sun Ragargaji Yan Bindiga Fiye da 45 a Zamfara

  • Sojoji sun ragargaji yan bindiga sama da 45 a wani harin sama da ƙasa da suka kai dajin Sabubu, jihar Zamfara
  • Rahotanni sun bayyana jami'an sojin Operation Hadarin Daji ne suka jagoranci kai samamen
  • Jirgin yakin sojin sama ne ya fara kai hari ta sama daga bisani dakarun sojin kasa suka karisa aikin ta kasa

Zamfara - Wani harin haɗin guiwa da sojojin sama da na kasa suka kai dajin Sabubu dake jihar Zamfara karkashin Operation Hadarin Daji ya sa an hallaka yan bindiga da dama.

Leadership ta ruwaito cewa an gano manyan yan ta'adda na ciki da wajen jihar sun taru a wani wuri da ake zargin maɓoyar kasurgumin ɗan bindiga, Halilu Tubali ne a arewacin dajin Sabubu.

Wani jami'in soji na sashin fasaha ya shaidawa PRNigeria cewa bayan samun bayanin taruwar su, nan take sojin sama suka kaddamar da kai hari dajin.

Sojoji sun shiga dajin sabubu a jihar Zamfara
Dakarun Sojoji Sun Kutsa Daji Ta Sama da kasa, Sun Ragargaji Yan Bindiga Fiye da 45 a Zamfara Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ya lamarin kai harin ya kasance?

Kara karanta wannan

An samar wa sojojin da ke yakar 'yan Boko Haram jirgin yawo lokacin hutu

Jami'in ya bayyana cewa an sanar da sojojin ƙasa dake kusa da dajin su kasance cikin shiri domin kai hari dajin da zaran an gama ruwan bama-bamai ta sama.

Jami'in yace:

"Ranar 6 ga watan Agusta, mun samu bayanin sirri cewa anga isar manya-manyan yan bindiga dajin daga cikinsu har da Halilu Tubali, ɗaya daga cikin manyan waɗanda ake nema."
"Cikin hanzari aka tura jirgin yakin Alpha zuwa wurin, da zuwansa ya hangi yan ta'addan sun yi shigar bakaken kaya. Nan take ya fara sakar musu bam a karon farko inda ya kashe su da yawa."
"Ragowar suka fara neman wurin ɓuya, amma jirgin ya sake sako bam karo na biyu a dai-dai inda ya fahimci suna ɓuya kuma nan take ya hallaka su."

Sojojin ƙasa sun isa wurin bayan harin sama

Rahoto ya nuna cewa ragowar da suka yi kokarin guduwa da manyan raunuka sun haɗu da sojojin ƙasa, inda suka karisa hallaka su.

Kara karanta wannan

Gwarazan Sojoji Sun Yi Gumurzu da Yan Boko Haram, Sun Ragargaje Su a Borno

Wannan harin yasa sojoji sun samu nasarar kashe fiye da yan bindiga 45 amma babu tabbas ko an kashe jagoransu Halilu Tubali.

Amma ɗaya daga cikin yan ta'addan da aka samu bai karisa mutuwa ba ya tabbatar da cewa harin sama ya yi kaca-kaca da mafi yawansu.

Duk wani kokarin na samun kakakin hedkwatar tsaro, Benjamin Olufemi Sawyer, domin tabbatarwa ya ci tura.

A wani labarin kuma An Tafka Ruwan Sama a Rana Daya da Ba'a Taba Irinsa Ba Cikin Shekara 100 a Katsina

A karon farko cikin shekara 100, an tafka wani mamakon ruwan sama a rana ɗaya fiye da yadda aka saba a Kastina

Shugaban NiMet, Farfesa Mansur Bako Matazu, shine ya bayyana haka a wurin taron kara wa juna sani a Abuja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A cewar Matazu, hukumar NiMet reshen Katsina ta gano cewa an zuba ruwan da ya kai milimita 100.

Kara karanta wannan

Jirgin NAF ya bankado yunkurin sace fasinjoji a babban titin Gusau, Zamfara

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262