Hukumar jin dadin alhazai ta yi kira ga maniyyata su dakatad da shirye-shiryen Hajjin bana

Hukumar jin dadin alhazai ta yi kira ga maniyyata su dakatad da shirye-shiryen Hajjin bana

Hukumar jin dadin alhazai NAHCON ta yi kira ga maniyyatan Hajjin bana da Umrah sun dakatad da duk wani shirye-shiryen ziyartar Makkah ko Madina har ila ma shaa’ llahu.

Kakakin hukumar NAHCON, Fatima Sanda, ta sanar da cewa an dakatad da shirye-shiryen Umrah zuwa kasar Saudiyya ne saboda matakin da kasa mai tsarkin ta dauka wajen kare kanta daga cutar Coronavirus.

Kawo yanzu, cutar ta yadu zuwa kasashe 48 kuma akalla mutane 82,164 sun kamu.

Mun kawo muku rahoton cewa Mahukunta a kasar Saudiyya sun hana maniyatta aikin hajji da Umrah shiga Makkah da Madinah domin gudun yada cutar Coronavirus da ke bazuwa a kasashen duniya.

Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Saudiyya ta ƙara da cewa za ta hana baki daga ƙasashen da aka tabbatar da bullar cutar ko inda ta ke barazana ga kiwon lafiyar mutane kamar yadda Bbc ta ruwaito.

Har ila yau, ma'aikatar a shafin ta na Twitter ta kuma ce da dakatar da amfani da shedar katin ɗan kasa a madadin fasfo a lokacin shiga da fita kasar ta Saudiyya.

Hukumar jin dadin alhazai ta yi kira ga maniyyata su dakatad da shirye-shiryen Hajjin bana
Hukumar jin dadin alhazai ta yi kira ga maniyyata su dakatad da shirye-shiryen Hajjin bana
Asali: Depositphotos

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Iran ta yi sanarwa ranar Alhamis cewa an dauki wasu sabbin matakan dakile yaduwar cutar Coronavirus da ta addabi kasar cikin makon nan.

Daya daga cikin matakan shine dakatad da Sallar Juma’a har ila ma sha’a llahu. Ma’aikatar ta bayyana cewa an haramta duk wani taron baja koli, khamsu-salawati, gidajen Sinima, bukukuwa, jana’iza, i’itikafi da duk wani gangami a kasar.

Shugaban sashen yada labaran ma’aikatar, Kianush Jahanpur, ya ce an kara yawan cibiyoyin gwajin cutar Coronavirus daga biyu zuwa bakwai, kuma za’a kara zuwa 15 kafin karshen makon nan, kuma 22 a makon gobe.

Hukumomin kasar Iran sun sanar a ranar Laraba cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar ya tashi zuwa 19 kuma mutane 139 suka kamu.

Bugu da kari, kasar Iran ta kulle dukkan makarantu, jami’o’i, cibiyoyin Ilimi a garin Qom da Arak.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng