Da Duminsa: Tankar mai ta fadi, ta nike mutane da dama a Ibadan
- Wasu fasinjoji sun rasa rayukansu yayin da tankar mai ta fadi a wani yankin jihar Oyo
- Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu an tattara mutanen da suka mutu zuwa asibiti
- Rahoto ya bayyana yadda lamarin ya faru, tare da bayyana rashin sa'ar ceto ko da mutum daya
Oyo - Akalla mutane biyar ne wata tankar mai ta murkushe a ranar Litinin a yankin Celica da ke kan sabon hanyar Ife zuwa Ibadan, karamar hukumar Egbeda a jihar Oyo.
Rahoton da Daily Nigerian ta wallafa ya bayyana cewa, tankar mai din ta kubce ne sannan ta kutsa kan wata karamar mota inda ta fada cikin ramin da ke kusa da motar.
Legit Hausa ta tattaro cewa, Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), Kwamandan sashi, Uche Chukwurah, ta tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021.
Misis Chukwurah ta bayyana hatsarin a matsayin mai muni, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar da suka hada da maza uku mata biyu manya.
Meye ya jawo hatsarin?
Kwamandan sashin ta bayyana cewa tankar ta samu matsalar birki ne, ta kubce sannan ta kutsa kan wata mota wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dukkan fasinjojin da ke cikinta.
A cewarta:
“Duk mutanen da ke cikin motar ta murkushe su har lahira kuma babu wanda aka ceto da rai.
Ta kara da cewa:
"An ajiye mamatan a dakin ajiyar gawarwaki na Asibitin Adeoyo."
Misis Chukwurah ta ci gaba da cewa jami’an hukumar kashe gobara suma suna wurin don hana barkewar gobara a yankin.
Yadda aka tsinci gawar wani jami'in JTF a karkashin gada a Abuja
A wani labarin, An gano gawar wani jami’in hadin gwiwa (JTF) a gadar Gwagwalada da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a babban birnin kasar.
Daily Trust ta gano cewa gawar jami’in, wanda ke sanye da kaki, ya huje da harbin harsashi. Matafiya sun gano gawar, wacce daga baya jami’an tsaro suka dauke ta, ranar Talata 3 ga watan Agusta, 2021.
Wani shaida, wanda aka bayyana sunansa da Gabriel, ya ce an gano gawar ne a gaban Otal din Brifina da ke Gwagalada.
Asali: Legit.ng