Yadda aka tsinci gawar wani jami'in JTF a karkashin gada a Abuja
- Wasu mazauna sun gano wata gawa ta wani jami'in JTF a karkashin gadar Gwagwalada a Abuja
- Rahoton ya bayyana cewa, da alamu an sace jami'in ne kafin daga bisani aka kashe shi aka jefar da gawarsa
- A halin yanzu an ruwaito cewa, rundunar 'yan sanda sun dauke gawar, suna kan bincike kan lamarin
Abuja - An gano gawar wani jami’in hadin gwiwa (JTF) a gadar Gwagwalada da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a babban birnin kasar.
Daily Trust ta gano cewa gawar jami’in, wanda ke sanye da kaki, ya huje da harbin harsashi.
Matafiya sun gano gawar, wacce daga baya jami’an tsaro suka dauke ta, ranar Talata 3 ga watan Agusta, 2021.
Wani shaida, wanda aka bayyana sunansa da Gabriel, ya ce an gano gawar ne a gaban Otal din Brifina da ke Gwagalada.
Ya ce daga baya wasu ‘yan sandan Gwagwalada sun tafi da gawar, wadanda suka zo wurin da motar sintiri.
Wata majiyar kuma ta ce mai yiwuwa an yi garkuwa da jami'in na JTF ne sannan daga baya wadanda suka sace shi suka kashe suka kuma jefar da gawarsa a kan babbar hanya.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ASP Maryam Yusuf, ta tabbatar da gano gawar amma ta ce mai yiwuwa jami’in ya yi hadari ne.
ASP Maryam Yusuf ta ce rundunar na bincike kan lamarin.
'Yan bindiga sun kai hari wani kauye, sun yiwa mai gari yankan rago
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari Okporo da makwabtanta a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.
Vanguard ta ruwaito cewa harin wanda aka fara a daren Lahadi, 1 ga watan Agusta ya ci gaba har zuwa safiyar Litinin, 2 ga watan Agusta.
Jaridar ta bayyana cewa har yanzu ba a san dalilin kai harin ba, inda ta kara da cewa mazauna garin sun danganta hakan da wasu gungun miyagu masu aikata miyagun laifuka da kuma wasu matsafa wadanda ke yin barna cikin dare.
Yadda 'yan sanda suka cafke wani da ake zargin yana karbar kudin fansa ta asusun banki
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a Suleja, Jihar Neja, ta cafke daya daga cikin wadanda ake zargin mai satar mutane ne da ke karbar kudin fansa ta banki a Babban Birnin Tarayya (FCT).
Wannan kenan kamar yadda mai asusun bankin da mai garkuwa da mutanen ya yi amfani da shi, Babawi Abba, ya dauki lauya don ya kare kansa domin ya tabbatar da cewa ba shi da laifi a cikin lamarin.
Daily Trust ta ruwaito cewa mijin daya daga cikin wadanda aka sace, Saheed Adewuyi cewa, ya biya N500,000 a cikin wani asusun bankin Access mai lamba 1403762272 da suna Badawi Abba Enterprise.
Asali: Legit.ng