Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan Neja a garinsa
- Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan labarai da dabaru na jihar Neja, Mohammed Idris
- Lamarin ya afku ne a daren ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta a kauyen Baban Tunga na karamar hukumar Tafa da ke jihar
- Sakataren gwamnatin Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ne ya sanar da wannan labarin
Neja - Rahotanni da ke fitowa daga jihar Neja na nuni da cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da kwamishinan yada labarai, Alhaji Sani Idris.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, sakataren gwamnatin Neja ne ya sanar da wannan labari mai tayar da hankali.
Matane ya ruwaito cewa an sace Idris ne a daren ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta a mahaifarsa, Baban Tunga, da ke karamar hukumar Tafa a jihar.
Ya ce har yanzu masu garkuwar ba su tuntubi juna ba, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Sai dai, ya bayyana cewa tuni jami'an tsaro suka fara bin sawun masu garkuwar, ya kara da cewa suna fatan ceto shi ba tare da wani rauni ba cikin kankanin lokaci.
Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda a jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na NAN faruwar lamarin sannan yayi alkawarin bayar da cikakken bayani nan gaba.
Babbar sakatariyar yada labaran gwamnan jihar, Mary Noel-Berje, ita ma ta tabbatar da ci gaban a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Ta ce:
"An bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Kwamishinan da misalin karfe 11 na daren jiya, Lahadi 9 ga Aug-2021, daga gidansa da ke kauyen Baban tunga a karamar hukumar Tafa ta Jihar.
“Hukumomin tsaro sun riga sun bibiyi 'yan fashin da nufin cafke su.”
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Jam'iyyar APC
A gefe guda, mun ji a baya cewa Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC na shiyyar C, Aminu Bobi, a yankin karamar hukumar Mariga, jihar Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace Bobi ne yayin da ya je gonarsa domin sanya ido ga masu masa aiki ranar Asabar da yamma.
Wata majiya dake kusa da wanda aka sace ya bayyana cewa maharan sun farmaki gonarne a kan mashina shida, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Asali: Legit.ng